1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsoron bullar murar tsuntsaye a Malawi

December 16, 2005
https://p.dw.com/p/BvGE

A yau din nan kasar Malawi ta aike da sanfurin jini da zuwa kasar Afrika ta kudu makwabciya, domin binciken kwayar cutar murar tsuntsaye,bayan an gano dubun dubatar tsuntsaya baki sun mutu a kan wani tsauni a tsakiyar lardin Tchisi.

Jamian kula da harkokin aikin gona sun baiyana tsoronsu,bayan mazauna kauyen sun fara kwasar matattun tsuntsayen suna miya da su a wannan mako.

Darektan kula da lafiyar dabbobi na amaikatar kula da lafiya ta kasar Wilfred Lipita,yace maaikatar ta aike da jamianta domin jan kunnen jamaa game da illar cin naman wadannan tsuntsaye,saboda akwai yiwuwar cewa suna dauke da kwayar cutar ta murar tsuntsaye wadda ta rigaya ta halaka wasu mutane a wasu kasashen .