1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsugune ba ta kare ba a Iraqi

Mansour BelloJune 17, 2004

Har kawo yanzu ana ci gaba da fafatawa da yan kunar bakin wake da dakarun kawance na Amurka a can Kasar ta Iraq

https://p.dw.com/p/Bviu
Motar daukar marasa lafiya zuwa Asibiti bayan hatsarin da ya rutsa da yan kasar ta Iraqi.
Motar daukar marasa lafiya zuwa Asibiti bayan hatsarin da ya rutsa da yan kasar ta Iraqi.Hoto: AP

A yau dai a ci gaba da yakin sunkuru a can kasar ta iraq wani dan kunar bakin wake ne ya tayar da bama bamai a cikin wata mota a kusaci da wani barikin soji a babban birnin kasar bagadaza inda yayi sanadiyar mutuwar a kalla mutane 35 tare da raunata wasu da dama .Wata majiya na cewa yan sari ka noken sun kara kaimi na tayar da fitina musamman a lokacin da ranar 30 ga wannan watan ke karatoowa na mika mulki ga yan kasar kamar yarda Amurka ta arkawarta ..Ministan kiwon lafiya na kasar ya tabbatar da cewa sama da mutane 138 ne suka sami munanan raunika a cikin wannan artabu .Daya daga cikin manyan sojojin Amurka a cikin kasar ta iraq yace an lalata daya daga cikin tankunan yaki na Amurka dake da kusaci da filin jirgin sama na Muthanna inda dakarun Amurkan sukai sansani ..Wannan lamarin dai ya faru ne a daidai lokacin da ake tantance wadanda ke neman shiga aikin soji a kasar ta iraq sai dai babu wanda hatsarin ya rutsa da shi .Wadanda suka ganewa idansu sun tabbartar da ganin gawarwaki a kann titin da abun ya faru a yayin da jamaa ke cikin dimuwa a sabili da wannan fashewar Bam din ..Wannan farmakin dai ya kasance na baya bayan nan a cigaba da dasa bama bamai a cikin kasar a daidai lokacin da Amurka zata mika ragamar mulkin kasar ga yan kasa zalla .A yayin da Pm iyad Allawi ya isa yankin da wanmnan hatsarin ya faru yqa bayyanawa yan kasar cewa a yanzu wasu tsiraru na neman dakale cigaba kasar ta kowace siga wanda kuma dole ne gwamnati ta fito domin yaki dasu yarda ya dace a nan gaba kadan ..To sai dai wata majiya na cewa yayan jamiyyar Baath ne magoya bayan sadam hussain ke cigaba da tayar da zaune tsaye a cikin kasar tare da goyan bayan yann kasashen ketare .A yanzu haka dai masu gudanar da wannan bore sun fara karkata ga fannin albarkatun kasar wato man fetur domin haifar da tsaiko na sayarwa a kasuwannin duniya ..Majiyar dai ta cigaba da cewa a yanzu ana cigaba da gyaran butun man da aka lalata a kudu da arewacin kasar a halin yanzu .A cikin wannan halin ne shugaba bush wanda ke fuskantar matsin lamba tare da kalubale daga kasashen ketare da kuma cikin gida kann manufofin kasar ta iraq yace zaa mayar da hankali kann tabbatar da kasancewar kasar tabi sahun sauran kasashen duniya ta fuskar yanayin zamanin da muke ciki da kuma zamantakewa ..To sai dai manya manyan sojojin kasar ta Amurka da jamian Diplomasiyya na sukan lamirin shugaba bush daya sanya kasar yaki da iraq kuma a yanzu ya haifar da koma baya ta fannin tasttalin arzikin kasa wanda a ganin su bai dace ba sam shugaba Bush ya nemi yin ta zarce a karo na biyu a mulkin kasar ..Tun daga jiya kawo yau dakarun Amurka ukku kenan suka mutu cikin wannan yamuutsi baya ga sauran yan kasashen ketare dake cikin dakarun hadin guiwwa a cikin kasar .Tun bayan da kifar da gwamnatin Sadam Hussain a shekarar data gabata a kalla sojojin Amurka sama da dari shidda ne suka bakunci lahira ..A wata takarda manyan sojojin na Amurka suka sanywa hannu su kimanin 27 sun tabbatar da tabarbarewar fannin tsaro a cikin gida baya ga haifar da zaman dar dar wanda a cewarsu suke neman Chanji wanda suka ce dole ne .Cikin wadannan jamian kuwa har da tsohon babban hafsan sojin kasar da kuma yayan jamiyyaun siyasar kasar biyu baya ga manyan jamian Diplomasiyya .Wadannan jamian dai sun sake nanata cewa Shugaba Bush na neman ya mayar da MDD tamkar wata mashawartar da bata da wani anfani a fagen siyasar duniya .To sai dai ministan harkokin kasar Colin Powell ya musanta cewa wai yakin Iraq ya mayar da Amurka tamkar saniyar ware a siyasar duniya kamar yarda wadannan jamian suka bayyana .