1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsugune tashin matasa a Faransa

Ibrahim SaniNovember 28, 2007
https://p.dw.com/p/CUKB

Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy na wata ganawar gaggawa da Jami´an Gwamnatinsa, don ɗaukar matakin daya dace kan tsageru, dake tashin zaune tsaye a ƙasar. Fitinar matasan a wasu yankunan birnin Faris, ta samo asaline bayan da wasu matasa biyu su ka rasa rayukansu, a hatsarin mota daya haɗa da motar ´Yan sanda na ƙasar. Jim kaɗan da dawowarsa daga wata ziyara a ƙasar Sin, Mr Sarkozy ya ziyarci Jami´an tsaron da su ka jikkata a faɗan taho mu gama, a tsakanin su da tsagerun matasan. A lokacin zanga-zangar rahotanni sun shaidar da cewa tsagerun, sun halaka ´Yan sanda biyu tare da jikkata wasu da dama. An dai bayyana wannan zanga-zanga, a matsayin mafi muni a ƙasar, a tsawon shekaru biyu da su ka gabata.