1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsunami a kudancin Asiya

December 29, 2004

Jamusawa masu yawan bude ido na daga cikin dubban mutanen da tsautsayin girgizar kasa da ambaliyar teku ya rutsa da su a kudancin Asiya

https://p.dw.com/p/Bvdw

A cikin jawabin da ya gabatar ministan harkokin wajen Jamus Joschka Fischer ya musulta girgizar kasar da ta haddasa ambaliyar teku a kudancin Asiya tamkar wani mummunan bala’i daga Indallahi da dan-Adam bai taba ganin shigensa ba a wannan karnin da muke ciki. Fischer bai ba da tabbatattun alkaluma a game da yawan Jamusawa da tsautsayin ya rutsa dasu ba, saboda har yau babu haske game da lamarin. Amma duk da haka ya ce Jamusawa sama da dari ne aka rasa makomarsu. Wannan maganar ta fi shafar yankin Khao Lak na kasar Thailand inda igiyar ruwa tayi awon gaba da wani otel, wanda akasarin bakinsa Jamusawa ne. Bayanai na kungiyar masu gidajen otel sun ce mutane 280 ne aka rasa makomarsu, wadanda suka hada da ma’aikata da kuma bakin da suka sauka a wannan otel mai suna Sofitel-Hotel a kasar Thailand. Bisa ta bakin ministan harkokin wajen na Jamus, wani jami’in diplomasiyyar kasar yayi shawagi a samaniyar yankin da bala’in ya rutsa da shi ta jirgin sama mai saukar ungulu, inda ya kara da cewar:

A wannan bangaren dai akwai barazana mai firgitarwa, ko da yake ba zamu iya ba da wasu tabbatattun alkaluma a halin nan da muke ciki yanzun ba. Fatanmu shi ne a samu da yawa daga cikin masu yawon bude idon da suka dare tudun na tsira. Amma a yanzun ba zamu iya tabbatar da hakan ba.

Matsalar ta kai intaha ta yadda ya zama tilas akan shugaban gwamnati Gerhard Schröder ya katse hutunsa domin komawa fadar mulki ta Berlin. Kazalika gwamnati ta tsayar da shawarar tura wasu jami’ai daga hukumar ‚yan sandan ciki, wadanda suka kware wajen gane gawawwakin matattu. An kuma tura jirgin saman sojan Jamus dake da asibitin tafi-da-gidanka zuwa Phuket ta kasar Thailand. A baya ga wasu jiragen saman guda biyu da aka tura zuwa kasar ta Thailand dauke da likitoci da magunguna da sauran kayan taimako, saboda su kwaso Jamusawa masu yawon bude ido zuwa gida. A kuma halin da ake ciki gwamnati ta kara yawan kudaden taimakon da ta ware domin yankunan da bala’in ya shafa zuwa Euro miliyan biyu. Fischer ya ce wannan lokaci ne da ya kamata a nuna zumunta ga mutanen da bala’in ya rutsa da su. Tuni aka kafa wani kwamitin da zai rika hada kan matakan taimako na KTT da sauran kungiyoyi na kasa da kasa da kuma na kasashen da lamarin ya shafa. Fischer yayi kira ga Jamusawa da su yi wa Allah da Ma’aiki su ba da taimakon kudi ga mutanen da bala’in ya rutsa da su a maimakon amfani da kudi wajen sayen rokokin nan na bikin shiga sabuwar shekara.