1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsungune ba ta ƙare ba a yankin Darfur

June 1, 2006
https://p.dw.com/p/Buvo

A yayin da wa´adin da ƙungiyar tarayya Afrika, ta ba ɓangarorin tawayen Sudan, da su ka ƙi sa hannu a kann yarjejeniyar birnin Abuja ya kai ƙarshe jiya,ƙungiyar tawaye JEM,ja jaddada matsayin ta, na ci gaba da gwagwarmaya.

Kakakin wannan ƙungiya, Mohamed Tirgani, ya bayyana cewa, yarjejeniyar, ba ta ƙunshi abun a zo a gani ba, da zai cenza rayuwar al´ummomin yankin Darfur.

Bugu da kari ya ce kungiyar sa ba ta shakkun takunkumin da Au za ta sarkafa mata.

A yayin da ya jawabi SalimAhmed salim wakilin Au a taronn sulhu ya bayana matukar takaici da matakin na kungiyar JEM.

Shima Hassan El Turabi da jam´iyar sa, ke da alaƙar ƙut da ƙut, da ƙungiyar tawyaen JEM, ya yi suka ga wannan yarjejeniya.

A taƙaice dai, za a iya cewa, har yanzu tsugune ba ta ƙare ba, a rikicin tawayen yankin Darfur.