1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsuntsaye Mafarauta

Abba BashirMarch 12, 2007

Bayani akan Tsuntsaye mafarauta masu idon hangen nesa

https://p.dw.com/p/BvUv
Mikiya
MikiyaHoto: International Union for conservation of nature

Jamaa masu sauraronmu assalamu alaikum, barkammu da wannan lokaci, barkammu kuma da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na wasikun ma su sauraro,shirin da yake amsa tambayoyin da ku masu sauraro kukan aikomana.

Tambaya: Fatawarmu ta wannan makon ta fito daga Malama Zahara’u Muhammad Isa, Birnin Yamai a Jamhuriyar Niger, Malamar cewa ta yi, Shin ta yaya tsuntsaye mafarauta, masu idon hangen nesa, irin su mikiya,suke iya hango abu daga wuri mai nisa,kuma ina so ku gaya min, ko suna iya hangen abu dakyau fiye da Dan-adam?

Amsa: Babu shakka Mafarautan tsuntsaye suna iya hangen abu dakyau fiye da Dan-adam, saboda suna da idanu karfafa wadanda suke taimaka musu su hango abu daga mafi nisan wuri yayin da suke farautar abincinsu. Allah ya haliccesu da manyan Idanu, kuma idanuwan nasu ,suna dauke da wasu kwayoyin halitta masu karfi da suke taimakwa gani, ma’ana dai suna gani sosai. Akwai kwayoyin taimakawa gani sama da miliyan daya a idanun tsuntsayen.

Mikiya dake tashi sama tsawon dubban mitoci,tana da karfin idon da zai iya hango abinda ke kasa daga wannan nisan duniyar. Kamar dai yadda jiragen yaki suke gano abokan gaba daga dubban mitoci, haka suma suke yiwa abincinsu, suna iya ganin launi komai kankantarsa ko kuma motsawarsa aban kasa. Idon mikiya na dauke a cibiyar maganai mikidarin dubu uku, kuma tana iya fadada abu sau shida ko takwas. Mikiya na fadada ganinta akan fili mai girman eka 30,000 yayin da take a sama tsawon mitoci 4,500. zasu iya bambance zomo dake boye a cikin ciyawa daga tsawon mitoci 1,500. ya tabbata cewa idon mikiya an halittar mata ne musamman saboda ita.