1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsuntsu mai rarake Bishiya

Abba BashirMarch 5, 2007

Yadda Tsuntsun woodpecker ya ke rarake bishiya

https://p.dw.com/p/BvUw
Tsuntsu mai rarake bishiya
Tsuntsu mai rarake bishiyaHoto: AP

Tsuntsu mai rarake Bishiya wato“woodpecker“,! Wata halitta ce daga nau’ukan tsuntsaye da Allah madaukakin Sarki ya halitta bisa hikima da ikonsa. Allah ya fi kowa sanin dalilinsa na halittar tsuntsu mai rarake Bishiya, to amma ba shakka akwai ayoyi da hikimomi masu yawa tattare da irin tsari na musamman da wasu mu’ujizozi da Allah ya kebanci wannan tsuntsu da su, wanda dole hankali ya yarda cewa Allah ya yi su ne don su zamo ayoyi, kuma abin lura da tunani ga mutane.

Tsuntsu mai rarake Bishiya ya samo sunansa ne daga aikinsa na rarake bishiya da tsinin bakinsa, kuma akwai nau’ika na wannan tsuntsu sama da 180 a Duniya.karar da ke samuwa yayin da tsuntsun yake rarake bishiyar, wata hanya ce ta isar da sako ga yan-uwansa da kuma sanar da sauran tsuntsaye cewar, wannan fa yankinsu ne.Har ila yau kuma wannan itace hanyarsa ta neman abinci, inda yake caccako kwari da kuma tsutsotsin da suke boye a cikin bishiya domin yayi kalaci.

Kowa ya sani cewa Tsuntsu mai rarake Bishiya, yana gina makwancinsa ne, ta hanyar rarake bishiya. Abinda mutane da yawa basa lura dashi shine, yadda woodpecker baya gamuwa da jirkitar kwakwalwa yayin da yake sassake bishiya da karfi da kansa. Abinda woodpecker yake yi yayi kama da mutumin da yake buga kusa a garu da kansa. Idan mutum zai samu kansa yana dukan kusa, lallai zai samu tabuwar kwakwalwa. Amma woodpecker, zai rarake bishiya mai kauri sau 38-43 a tsakanin minti 2.10 da 2.69 kuma babu abinda ya same shi.

Babu abinda zai faru saboda an halicci kan woodpecker ne don yayi irin wannan aiki. Kwanyar woodpecker tana da wani irin tsari da yake rage ko jure karfin kaurin bishiyar. Yana da wasu tausasan kasusuwa na musamman a cikin kwanyar.