1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tuhumar harin taáddanci a ƙasar Amirka

Abdullahi Tanko BalaFebruary 12, 2008

Hukumar tsaron Amirka Pentagon ta buƙaci aiwatar da hukuncin kisa akan waɗanda ake tuhuma da harin 11 ga watan Satumba a Amirka

https://p.dw.com/p/D6C7
Khalid Sheikh Mohammed, jagoran harin 11 ga watan Satumba akan ƙasar AmirkaHoto: AP

Wannan dai shine karon farko tun kusan shekaru shida da rabi da aukuwar harin na 11 ga watan Satumba da hukumar tsaron ta Amirka ta gabatar da tuhumar mutanen shida a gaban kotu a hukumance. Ta kuma tattara bayanai da hujjoji 170 domin tabbatar da laifin da ake tuhumar mutanen da aikatawa.

Maáikatar tsaron ta ce zata buƙaci kotun sojin ta yanke hukuncin kisa akan mutanen shida bisa laifukan da suka haɗa da haɗin baki da kisan kai da kai harin akan jamaá fararen hula da kuma ɗaurewa taáddanci gindi waɗanda tace dukkanin su sun saɓa da dokar yaƙi.

Mutanen shida da ake tuhuma sun haɗa da Khalid Sheikh Mohammed wanda ya aiyana kan sa a matsayin mutumin da ya shirya kai harin mafi muni na 11 ga watan Satumba a ƙasar Amirka. Birgediya Janar Thomas Hartmann mai bada shawara ga maáikatar tsaron Amirka wanda ya gabatar da laifin da ake tuhumar mutanen da aikatawa yace harin taáddancin ya yi sanadiyar mutuwar mutane 2,974 wannan ya sa ya zama wajibi ga kowanne daga cikin mutanen su ya fuskanci hukunci mai tsanani sakamakon abin da suka aikata.

Birgediya janar Thomas Hartmann ya kuma ƙara da cewa Khalid Sheikh Mohammed shine babban wanda ya kitsa kai harinn na 11 ga watan Satumban 2001, yana mai cewa Kahlid Mohammed shine ya gabatarwa Osama bin Laden tsarin yadda zaá aiwatar da harin a shekarar 1996, inda kuma ya sami goyon baya da maƙudan kuɗaɗe daga Osama domin aiwatar da harin tare da bada horo ga yan taáddan a ƙasashen Afghanistan da Pakistan.

Waɗannan bayanai dai hukumar leƙen asiri ta Amirka CIA ta tatso su ne daga tuhumar da ta yiwa mutanen a yayin da ake tsare da su a sansanin Guantanamo. Sai dai abin da ake jiran fayyacewa a gaban kotu shine ko an tursasawa mutanen wajen tatsar waɗannan bayanai. Ƙungiyoyin kare haƙƙin bil Adama sun yi zargin cewa jamian leƙen asiri sun yi amfani da matakan azabtarwa waɗanda suka saɓawa ƙaída musamman akan Khalid Sheikh Mohammed wajen tatsar bayanai.

Ita ma dai ƙungiyar kare haƙƙin bil Adama ta Human Rights watch, tace ko da yake ya dace a hukunta waɗanda suka aikata harin taáddancin na 11 ga watan Satumba, amma bai halasta a hukunta su a ƙarƙashin tsari mara adalci na kotun soji ba. Ko da yake dai baá baiyana takamammen lokacin da Kotun zata fara sauraron shariár ba, manazarta na ganin zaá ɗauki tsawon watanni kafin a kammala.