Tuhumar Kotu ta masu hannu a rikicin Jos
April 1, 2010Wata kotu a birnin Jos ta tuhumi mutane 20 da laifin ruruta wutan rikicin ƙabilanci na kwanakin baya, da ya haifar da salwantar rayukan ɗaruruwan mutane a Jihar Plateau. An ɗage zaɓen har i zuwa 15 ga wannan wata na Afrilu, bayan da ɗaukinsu suka ƙi amsa laifin da ake tuhumesu da aikatawa. Sai dai ana ganin cewa za a shafe watanni kafin a yanke hukuncin farko, sakamakon tafiyar hawainiya da harkokin shari´a suka saba yi a tarayyar ta Nigeria. Idan dai an same su da laifin da ake zarginsu da aikatawa, za a iya yanke musu hukuncin kisa.
Mutane 162 ke hannun jami´an tsaro a halin, amma kuma 41 daga cikinsu ne za a gurfanar gaban ƙuliya bisa zargin kisan kai da kuma aikin tarzoma. Ana ganin cewa hukumomin Nigeria na so su yi amfani da shari´ar wajen kawo ƙarshen jain ja da yana asalin Jos da kuma ƙabilar hausa-fulani ke yi.Rikicin na jihar Plateau da ya ƙi ci yaƙi cinyewa, ya sa tarayyar Nigeria ta yi ƙaurin suna a duniya a fiskar yakin ƙabilanci da kuma na addini.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Zainab Mohammed Abubakar