1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tungar Boko Haram ta zama filin atisayen sojoji

March 27, 2017

Runduar Sojin Najeriya za ta fara wani  atisayen gwajin makamai a dajin Sambisa inda sojin kasar za su gwada karfin su, da kuma yi gwajin barin wuta da makaman yaki na sojin kasa da kuma bindigogin atilare.

https://p.dw.com/p/2a3df
Nigeria Notstand Islamisten Truppen Armee Soldaten
Hoto: picture-alliance/dpa

Tun lokacin da Sojojin Najeriya suka ayyana karbe iko da wurin da suka kira babban sansani da ya saura na mayakan Boko Haram a dajin Sambisa, babban hafsan Sojojin Najeriya  janar Tukur Yusuf Buratai, ya sanar da cewa a cikin wannan shekarar za a yi atisaye na gasar gwajin makamai a dajin an Sambisa. Bisa hakan a wannan Litinin ne runduar sojojin ta fara wani atisayen gwajin makamai a dajin wanda a baya ke zama matattaran 'yan ta'adda. Inda sojin kasar za su gwada karfinsu da kuma yin gwajin barin wuta da makaman yaki na sojin kasa da kuma bindigogin atilare.

Wannan dai shi ne karo na farko da rundunar sojoji da za ta gudanar da irin wannan atisaye na gasar gwajin kananan makamai a wannan daji, wanda ake kokari na tabbatar da iko da ta ke da shi kan dajin, bayan karbe shi daga ikon Kungiyar Boko Haram.
Masana tsaron dai na kallon wannan mataki da sojojin suka dauka na tabbatar da nasarar da suka samu a yaki da ake yi da Kungiyar Boko Haram tsawon shekaru bakwai.

Aliyu Hussaini, wani tsohon jami'in tsaro ya ce wannan gasar gwajin makamai da sojoji suka fara na tabbatar da cewaNajeriya ta samu nasarar yaki da kungiyar, saura kasashen makobta su kammala da na wajajen su. Shi ma dai Sharif Garba Ibrahim, mai fashin baki kan harkokin yau da kullum dai, yana cikin wadanda suka buka ci wannan nasara da ake cewa an samu a fadada ta zuwa yankunan da har yanzu suke fama da kalubalen tsaro da sauran dazukan da ake ganin 'yan kungiyar na boye a ciki.

Rundunar sojojin ta yi bayanin cewa atisayen dai zai kunshi gasar harbin manya da kanan makamai, tsakanin rundunonin sojojin dabam-dabam, inda ake sa ran zai karfafa basirar sojojin da kara fahimtar dabarun yaki da ma na sarrafa makaman zamani.