1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tura dakaru zuwa Kongo

March 7, 2006

Kungiyar Hadin Kan Turai na shawarwari na tura dakarunta zuwa kasar Kongo, don taimaka wa rundunar kare zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya tabbatad da tsaro a lokacin zaben kasar da za a gudanar a cikin watan Yuni mai zuwa.

https://p.dw.com/p/Bu1H
Dakarun kare zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a kasar Kongo.
Dakarun kare zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a kasar Kongo.Hoto: AP

A wannan shekarar ne, karo na farko da za a gudanad da zaɓen dimukraɗiyya a Jumhuriyar Dimukraɗiyya Ta Kwango, tun shekaru 46 da suka wuce. Babu shakka wannan shirin na ɗauke da kasada, saboda tun 1960, yayin da ƙasar Belgium, wadda ta yi wa Kwangon mulkin mallaka, ta janye daga ƙasar ne, rikici ya ɓarke, wanda kuma har ya zuwa yanzu, ya ƙi ci ya ƙi cinyewa. An dai yi ta yaƙe-yaƙen basasa tun da ƙasar ta sami `yancinta daga Belgium. Amma yaƙin basasan da ya fi muni a Kwangon, shi ne na 1998 zuwa shekara ta 2003, inda fiye da mutane miliyan 3 suka rasa rayukansu. Har ila yau dai a kan sami fafatawa tsakanin `yan tawaye da dakarun gwamnati a gabashin Kwangon.

Tun shekara ta 2001 ne kuma shugaban ƙasar na yanzu, Joseph Kabila, ya hau karagar mulki, bayan da aka yi wa ubansa, Laurent Kabila, kisan gilla a wani yunƙurin juyin mulkin da aka yi. To a zaɓen da ake shirin gudanarwa a cikin watan Yunin wannan shekarar, shi Joseph Kabilan na neman tabbatad da ikonsa ne da kuma zarcewa a kan karagar mulki. Sai dai, gwamnatin da yake shugabanci yanzu, ta haɗin gambiza ce, wadda kuma ta ƙunshi madugan `yan tawayen ƙasar. Bisa dukkan alamu dai, waɗannan madugan ba su da wata hanyar samun nasara a zaɓen.

Sabili da haka, mai yiwuwa ne bayan zaɓen, za su koma daji su ta da wani rikicin kuma, don dai su ga cewa ko ta yaya, sai an dama da su.

Ulrich Delius, wani masani ne kan harkokin Kwangon, wanda kuma a halin yanzu yake aiki da wata ƙungiya mai fafutukar kare hakkin `yan tsiraru a duniya. Game da halin da ake ciki a Kwangon dai, ya bayyana cewa:-

„Akwai tsoffin madugan `yan tawaye da dama, waɗanda a halin yanzu ke cikin gwamnatin Kwangon, suke kuma riƙe da muhimman muƙamai. To idan son su ne, kamata ya yi a ci gaba da yadda ababa sukke a halin yanzu. Wato ke nan, inda gwamnatin tsakiya ba ta da wani cikakken ikon zartaswa, sa’annan kuma gwamnonin jihohi da madugan `yan tawayen ke abin da suka ga dama a yankunan da suke da angizo.“

Sau da yawa dai, an sha ɗaga lokacin zaɓen Kwangon. A tsakiyar watan Yunin wannan shekarar ne aka tsai da lokacin gudanad da sabon zaɓen, wato idan ba a sake daga shi ba.

Tun 1999 ne dai dakarun kare zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya da aka girke a ƙasar, ke yunƙurin tabbatad da ganin cewa an kiyaye ƙa’idojin tsagaita bude wuta. A yanzu dai, rundunar, wadda ta ƙunshi dakaru dubu 18 da ɗari 6 da kuma fararen hula da dama da ke aiki ƙarƙashinta, ita ce tawagar kare zaman lafiya ta Majalisar Ɗinkin Duniya mafi girma a duniya baki ɗaya. Bini bini dai, a kan sami ɓarkewar fafatawa tsakanin dakarun da mayaƙan `yan tawaye a gabashin Kwangon.

Don dai tabbatad da cikakken tsaro a lokacin zaɓen ne Majalisar Ɗinkin Duniya ta bukaci Ƙungiyar EU da ta taimaka da sojoji, waɗanda bisa dukkan alamu, za a tura ne zuwa gabashin Kwangon. Ko wane irin ɗauki za su yi a wannan yankin ?

Hans-Georg Ehrhart, wani jami’i ne a cibiyar nazarin fauftukar samad da zaman lafiya da tabbatad da tsaro, ta birnin Hamburg. Game da wannan tambayar, ya bayyana cewa:-

„A zahiri dai, abin da ake son a cim ma shi ne, hana duk wani yunƙurin da madugan yaƙin, waɗanda a halin yanzu ke cikin gwamnatin Kwangon, za su yi bayan zaɓen, idan sun sha kaye, na sake komawa daji su fara yaƙin sunƙuru.“

Ita dai Majalisar Ɗinkin Duniya, ta bukaci taimakon sojoji ɗari 8 ne daga Ƙungiyar EUn. Manazarta al’amuran yau da kullum na ganin cewa, wannan ba wani abin da zai gagari ƙasashen ƙungiyar ba ne, musamman ma dai idan aka yi la’akari da cewa, da can babu abin da suka taɓuka wajen kare zaman lafiya a Kwangon.