1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turai ta buƙaci cire shingayen hana isa Gaza

June 1, 2010

Turai da Rasha suka ce, babu wata hujjar da za ta iya kare harin da Isra'ila ta kai akan wasu jiragen agaji ga Falasɗinawa

https://p.dw.com/p/Nenv
Hoto: AP

Ƙungiyar tarayyar Turai EU da kuma ƙasar Rasha, waɗanda suma suka bi sahu wajen yin Allah wadai da harin da Isra'ila ta ƙaddamar akan wasu jerin jiragen ruwa da ke ɗauke kayayyakin agaji zuwa zirin gaza na Fasɗinawa sun yi ƙira ga cire ɗaukacin shingayen dake hana kaiwa yankin domin bada damar isar da kayayyakin agajin bil'adama. A cikin wata sanarwar haɗin gwiwar da Rasha da tarayyar Turai suka fitar bayan wani taron da suka gudanar a birnin Rostov - on - Don dake kudancin Rasha, ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov da kuma kantomar kula da harkokin wajen tarayyar Turai Catherin Ashton, sun kuma buƙaci gudanar da cikakken bincike - ba tare da nuna wani son kai ba. Shugaban Rasha Dmitry Medvedev ya shaidawa wani taron manema labarai tare da shugabannin tarayyar Turai cewar, ba za'a iya mayar da rayukan da suka salwanta ba kuma babu wata hujjar da za ta iya kare matakin da Isra'ilar ta ɗauka. Shima shugaban majalisar tarayyar Turai Herman Van Rompuy, cewa yayi babu wani dalilin da zai halatta ƙaddamar da harin. A halin da ake ciki kuma, shugaba Husni Mubarak na ƙasar Masar ya bayar da umarnin buɗe kan iyakar Rafa domin kai kayayyakin agaji a zirin na gaza.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Umaru Aliyu