1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turai ta soki matakin nada Boris Johnson

Gazali Abdou TasawaJuly 14, 2016

Wasu kasashen Turai da suka hada da Faransa da Jamus sun nuna rashin gamsuwarsu da matakin nada Boris Johnson a matsayin ministan harkokin waje a sabuwar gwamnatin Birtaniya

https://p.dw.com/p/1JOu8
Großbritannien Boris Johnson Außenminister
Hoto: Reuters/A. Matthews

Kasashen Turai sun soma yin suka dama bayyana takaicinsu da matakin nadin ba zata da sabuwar Firaministan Birtaniya Theresa May ta yi wa Boris Johnson wanda ya jagoranci masu ra'ayin ficewar Birtaniya daga kungiyar Tarayyar Turai EU, a matsayin ministan harkokin kasashen ketare cikin sabuwar gwamnatin kasar. Martani na farko dai ya fito ne daga ministan harkokin wajen Faransa Jean-Mark Ayrault wanda ya zargi Boris Johnson din da zabga karya a lokacin yakin neman zaben raba gardama kan batun ficewar Birtaniya daga kungiyar ta EU, dan haka ya ce ya so a ce an samar masu da abokin aiki mai kima da daraja. Shima dai daga nashi bangare takwaransa na Jamus Frank-Walter Steinmeier, ya bayyana takwaransa na Birtaniyar a matsayin maras alkibla.