1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turai: Tsaurara matakan tsaro bayan harin Brussels

Yusuf BalaMarch 22, 2016

Shugabannin kasashen duniya na ci gaba da jajanta wa ga al'ummar Beljiyam bayan harin da aka kai filin sauka da tashin jiragen sama da ma tashar jiragen ƙasa.

https://p.dw.com/p/1IHgv
Frankfurt Flughafen Polizei Sicherheitsvorkehrungen nach Terroranschlägen in Belgien
Hoto: picture-alliance/AP Photo/M. Probst

Harin da ke faruwa kwanaki bayan kama Salah Abdesalam da ke da hannu cikin harin da aka kai a birnin Paris a watan Nuwambar bara ya shiga hannun mahukunta, kamun da aka yi masa a birnin Brussels bayan da a ke ta yabawa jami'an tsaro na wannan kasa ta Beljiyam, a ɓangare guda kuma an riga gargaɗin cewa an tsaurara matakan tsaro sai ga shi da sanyin safiyar nan ta Talata an kai hari a filin tashi da saukar jiragen sama na Brussels da tashar jirgin ƙasa ta Maelbeek wacce ba ta da nisa da inda majalisar Tarayyar Turai ke zama a Brussels.A cewar Firaministan Birtaniya David Cameron wannan hari na Beljiyam tamkar kai hari a ƙasashen Turai ne.

"Waɗannan hare-hare ne a Beljiyam na iya zama tamkar hare-hare ne da aka kai a Birtaniya ko Faransa ko Jamus kowani ɓangare na ƙasashen Turai ɗan haka dan dole ne mu haɗa kanmu dan ganin cewar 'yan ta'addar ba su sami dama ba ta yin nasara dan haka ne muke ɗaukar matakai da jami'an tsaro na ƙasar ta Beljiyam dan mu tabbatar da ganin dakarun tsaronmu suna aiki tare".

Wani da lamarin ya shafa Alexandre Brans dan shekaru 32, wanda ke a cikin jini sakamakon harin ya ce jirgin ƙasa na daf da barin wannan tasha sai kawai suka ji ƙara mai karfin gaske inda mutane suka shiga ruɗani. An dai buƙaci fasinjoji da ke son zuwa filin tashi da saukar jiragen saman da su ƙaurace masa.Firaministan na Birtaniya ya ce wannan hari ya sanya ƙasarsa ta sake tsaurara matakanta na tsaro.

" Na jagoranci zaman taron COBRA a nan London muna yin duk abin da ya dace dan sake bai wa kanmu kariya dan haka za'a ga ƙarin dakarun tsaro a kan iyakokinmu na ruwa da filayen tashi da saukar jiragen sama da tashoshin jiragen ƙasa, amma wannan lokaci ne mai wahala da 'yan ta'adda suka sakomu a gaba suke neman rayuwarmu suke kai mana hari dan sanin matsayinmu dan haka muma ba za mu bari ba siu yi nasara".

Shi kuwa shugaban ƙasar Faransa Francois Hollande ya bayyana wannan rana a matsayin bakar rana.Wata kafar yada labarai ta VRT ta ce mutane mutane da suka rasu a filin tashi da saukar jiragen saman sun kai 35 yayin da waɗanda suka samu raunika suka haure 170.Jami'an tsaro daga Amirka na cewa ta yi wu an shiga filin tashi da saukar jiragen saman ne cikin akwati irin ta matafiya.FBI na aiki tare da jami'an tsaro na Beljizam dan bincike kan wannan hari da aka kai .