1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turai za ta hana yaɗuwar rikicin tattalin arziƙin Girka .

May 8, 2010

Shugabannin Turai suka ce zasu tabbatar da kare martabar takardar Euro.

https://p.dw.com/p/NJAn
Hoto: picture alliance / dpa

Shugabannin ƙasashen dake amfani da takardar kuɗi ta Euro waɗanda suka gudanar da taro cikin dare a birnin Brussels, hadikwatar tarayyar Turai sun amince da baiwa ƙasar Girka ɗauki saboda rigimar tattalin arziƙin data shiga. Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da shugaban Faransa Nikolas Sarkozy, sun ƙara da yin ƙira ga bayar da wani tallafin gaggawa ga wani asusun da zai taka rawa wajen hana fuskantar matsalolin da ke da nasaba da ɗimbin bashin da zai dabaibaye wata ƙasa. Akan hakane kuma ministocin kula da harkoki kuɗi a ƙasashen na Turai, zasu gudanar da wani taro a gobe Lahadi - idan Allah ya kaimu domin tsara irin matakan da za su ɗauka da nufin yaƙi da rashin tabbas ɗin da kasuwannin hada hadar kuɗi ke yi akan Euro. Shugaba Sarkozy ya ce, idan har aka sake buɗe kasuwannin hada hadar a ranar Litinin, to kuwa a shirye Turai take ta kare takardar kuɗi ta Euro.

Shi kuwa shugaban hukumar tarayyar Turai Hose Manuel Barroso, cewa ya yi dukkan sassan da lamarin ya shafa sun cimma matsaya akan buƙatar kare takardar Euron:

" Batun dake muhimmamcin da dukkan ɓangarori suka yi na'a da shi, shi ne na yin iya iyawar mu wajen bada kariya ga darajar kuɗin Euro. Muna da zaɓi daban daban, kuma za mu yi amfani da su."

Mawallafi: Saleh Umar Saleh