1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turai za ta yi taro kan 'yan gudun hijira

Pinado Abdu WabaAugust 30, 2015

Kasashen Turai sun ce adadin 'yan gudun hijiran shi ne mafi yawa da aka taba gani tun bayan yakin duniya na biyu.

https://p.dw.com/p/1GOFO
Frankreich Innenminister Thomas de Maiziere in Paris
Ministan cikin gidan Jamus Thomas de MaiziereHoto: picture-alliance/dpa/E. Laurent

Ministocin cikin gidan Jamus da Faransa da Birtaniya sun yi kira ga kasashe 28 da ke kungiyar Tarayyar Turai da su gudanar da wani taro na musamman dangane da tudadowan 'yan gudun hijira, abin da ke kasancewa nahiyar karfen kafa a wannan lokaci.

Wannan ya zo ne bayan da aka sami labarin cewa an harbe wani matashi dan gudun hijira, mai shekaru 17 na haihuwa, yayin da yake kokarin shiga Girka.

Da ma bisa tsarin Kungiyar Tarayyar Turan, sai ranar takwas ga watan Oktoba mai zuwa ministocin cikin gidan za su gana, yanzu sun sanya ranar 14 ga watan Satumba mai kamawa sannan sun bukaci da a gaggauta rajistan bakin da daukar hotunan yatsun su saboda a iya tantance masu bukatar mafaka, saboda yanayin kasashensu, da ma jerin kasashen da za a iya kai musu masu gudun hijira ba tare da sun fuskanci wani hadari ba