1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hana ayyukan kungiyar Hizmet ta Gülen

Uwais Abubakar Idris/LMJJuly 30, 2016

Ana ci gaba da nuna 'yar yatsa a kan kungiyar Hizmet ta Fethullah Gülen a kan batun yunkurin juyin mulkin kasar Turkiyya da bai samu nasara ba.

https://p.dw.com/p/1JYqV
Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan da shugaban kungiyar Hizmet Fethullah Gülen
Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan da shugaban kungiyar Hizmet Fethullah GülenHoto: Links: picture-alliance/dpa/AP/Pool // Rechts: Reuters/Handout

Kungiya ta Hizmet dai ta yi ficce a fannin ilimi musamman a kasashe irin na Najeriya. A shekarar 1998 ne kungiyar ta Hizmet ta fara gudanar da harkokinta a Najeriya inda ta fi mai da hankali a fannoni ilimi da taimakawa marasa galihu da kuma sasantawa tsakanin alumma, musamman mabiya addinai. Kamar yadda take yi a kasashe fiye da 160 da take gudanar da harkokinta, a Najeriyar ma fannin ilimi ya kasance muhimmi abu da Hizmet ta mai da hankali inda take da makarantu 18 tun daga matakin nursery har zuwa matakin jami'a. Shin me ya dauki hankalin wannan tafiya karkashin Fethullah Gülen ne zuwa ga fannin na ilimi a kasa irin Najeriya? Jamal Yigit jami'i ne a cibiyar ta Hizmet da ke Abuja.

Ya ce: "Mun damu ne da harkar ilimi sanin cewa ilimi zai kara wanzuwar zaman lafiya a tsakanin kasashe. Don haka muka yi dabarar bude makarantu masu zaman kansu bisa manufar samar da daliban da zasu zama wadanda suka yi fice a al'ummunsu. Don ta fanin ilimi ne za a kyautata rayuwar al'umma su samu fahimtar junansu ta hanyar da ta dace"

Yunkurin kifar da gwamnati a turkiya bai yi nasara ba
Yunkurin kifar da gwamnati a turkiya bai yi nasara baHoto: Reuters/U. Bektas

Taimako a fannin ilimi a kasashe da dama

Bisa la'akari da irin karfin fada a ji da ya sanya daukaka fanin ilimi a matsayin daya daga cikin muhimman ayyukan Hizmet a kasashe da dama, ta hanyar ilimi a kasa irin Najeriya da harkokin ilimi suka kasance cikin mawuyacin hali, ya sanya duba shin wane tasiri ayyukan Hizmet suka yi ga harkokin ilimin Najeriya? Bincike dai ya tabbatar da cewa cibiyar Hizmet ta kasar Turkiya karkashin Gülen na bada guraben karo ilimi har 20 ga dalibai da ke karatu a Najeriya da ma kasar ta Turkiya.

Kodayake jami'an ma'aikatar ilimin Najeriya sun ki cewa uffan a kan yadda suke kalon ayyukan Hizmet a fanin ilimi saboda takaddamar da jagoranata Fethullah Gülen ke ciki a game da zargin hannu a yunkurin juyin mulkin na Turkiya, a bayyane take a fili irin tasirin da Hizmet ke da shi a tsakanin al'umma a kasashe fiye da 160 ciki har da Najeriya.