1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiya ta buƙaci Iraƙi da ta rufe sansanonin ´yan tawayen ƙungiyar PKK

October 20, 2007
https://p.dw.com/p/Bu8B

FM Turkiya Recep Tayyip Erdogan yayi kira ga gwamnatin Iraqi da ta rufe sansanonin da ´yan tawayen Kurdawa ke amfanin da su dake arewacin Iraqin. Hakazalika gwamnati a birnin Ankara ta nemi takwararta a Bagadaza da ta mika mata shugabannin kungiyar Kurdawa ta PKK. A ranar laraba da ta gabata majalisar dokokin Turkiya ta bawa dakarun kasar ikon yin kutse cikin arewacin Iraqi don farautar ´yan tawaye wadanda ke amfani da wannan yanki suna kaddamar da hare hare a cikin Turkiya. Gwamnatocin biranen Bagadaza da Washington sun yi kira ga Turkiya da ta guji daukar matakan soji suna masu cewa hakan zai haddasa rudani a yankin baki daya.