1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiya ta haye matakin farko a batun samun karbuwa cikin Kungiyar TaraiyarTurai

Hauwa Abubakar AjejeOctober 4, 2005

Kungiyar ta Turai ta amince tattauna batun karbar Turkiya a matsayin cikakkiyar memba,bayan adawa da wasu kasashe membobi suka nuna

https://p.dw.com/p/BvZE
Shugaban Turkiya Tayyib Erdogan
Shugaban Turkiya Tayyib ErdoganHoto: AP

An samu jikirin bikin bude taron,har zuwa cikin dare a jiya litinin,bayan mahawara ta kwanaki biyu akan kin amincewa da Austria da kuma Turkiya suka yi da shawarar da Kungiyar Taraiyar Turai ta bayar akan batun shigar Turkiyan cikin kungiyar,wanda hakan ya baiyana irin rashin yarda dake tsakanin bangarorin biyu.

Ministan harkokin waje na Turkiya Abdullahi Gul,da yake baiyana farin cikinsa a game da matsaya da aka cimmawa,ya nanata kalaman da gwamnatin Turkiyan takeyi a baya cewa,shigarta cikin kungiyar,zata cike gibi dake akwai a tsakanin musulmi da kirista zai kuma taimaka kawo karshen tashe tashen hankula dake da alaka da kungiyoyin islama.

Ministan harkokin wajen Burtaniya Jack Straw,bayan nuna gamsuwarsa game da wannan mataki,ya kuma bukaci Turkiya da ta itama ta dauki nauyi daya rataya wuyanta na bin dokokin kungiyar,kodayake yace har yanzu da sauran rina a kaba a batun shigar Turkiya kungiyar saboda wasu matsaloli na dabam,wadanda kuma suka kunno kai, ko da wajen taron na jiya,inda ministan harkokin wajen wajen Turkiya Abdullahi Gul ya wuce kai tsaye zuwa kujerersa a lokacinda ya shiga zauren taron,yana mai ketare ministocin harkokin wajen kasashen,Austria da Cyprus wadda Turkiyan bata amince da ita ba,ba tare day a gaisa da su ba.

Kasar Amurka ta shiga tsakani,inda ta nuna goyon bayanta,wadda kasar Austria ta amince bayan adawa da ta yi da kasancewar Turkiya cikakkiyar memba ta kungiyar,batu da kungiyoin siyasa musamman na masu tsatsauran raayi da na Christian Democrats na yankin basa kauna.

Kungiyar ta Taraiyar Turai mai membobi 25, a nata bangare tace karbar Turkiya cikinta ya dogare ne musamman akan kokarin Turkiyan na kare yancin bil adama da sukayi dai dai da kaidojin kungiyar da kuma sauran batutuwa dabam.

Ba tare da an cimma yarjejeniyar fara taron na yau ba kuwa,da zai kawo cikas ga sauye sauyen siyasa,da saka jari na waje a kasar Turkiya,tare da munana rikicin yankin musaman bayan kin amincewa da daftrin tsarin mulkin kungiyar da kasashen Faransa da Netherlands suka yi.

Ministan harkokin wajen Portugal yace wannan shawarar zata matukar batawa Osama bin Laden rai,saboda kira da kungiyarsa ta Alqaeda takeyi na kare yaduwar aladun kasashen yammacin duniya da yada akidar Islama a kasashen musulmi.

Kasar Turkiya mai yawan jamaa miliyan 72,a halin yanzu tana fuskantar namijin aiki na yin koyi da tsare tsaren siyasa,tattalin arziki da halin rayuwa irin na Turai,tare kuma da kaddamar da dokokin Kungiyar Taraiyar Turai masu shafuna dubu tamanin.

Ana sa ran zaa kawashe kusan shekaru 10 ana tattuna wannan batu,ga shi kuma kasashen Austria da Faransa sun alkawartawa yan kasarsu cewa suke da ikon yanke shawarar karshe cikin kuriar raba gardama da zaayi akan batun karbar Turkiya cikin Kungiyar Tariyar Turai.