1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiyya na shirin keta umurnin Jamus

March 19, 2017

Bisa ga dukkan alamu gwamnatin Turkiyya na shirin yin gaban kanta kan jin ra'ayin Turkawa mazauna Jamus da aka ki amince mata.

https://p.dw.com/p/2ZVKp
Türkei Erdogan Rede im Bestepe Zentrum in Ankara
Hoto: picture-alliance/abaca/AA/M. Ali Ozcan

Ministocin kasar Turkiyya na shirin gudanar da gangami a kasar Jamus don neman ra'ayin Turkawa a kuri'ar jin ra'ayin da ake shirin yi dangane da gyaran kundin tsarin mulkin kasar da zai baiwa Shugaba Rajab Tayyib Erdogan karin karfin iko. Wannan yunkuri dai zai iya ruruta wutar rikicin da ke tsakanin Turkiyyar da Jamus.

Turkiyya dai na cacar baki a yanzu da kasashen Jamus da Holland, wadanda suka hana ta gudanar da wadannan gangamin neman ra'ayin turkawa mazauna kasashen nasu, saboda da tsoro irin na tsaro.

Cikin wata hira da tashar talabijin ta CNN, wani kakakin Shugaba Erdogan, Ibrahim Kalin, ya amince cewar fargaba kan Turkiyya na karuwa tsakanin kasashen Turai, sai dai ya yi ikirarin cewa Turkiyyar dai na matsayin kasar da ke da saukin huldar arziki ga masu bukatar harka ta saka jari.