1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiyya ta yi tir da hukuncin da aka yanke wa dan kasarta

Mohammad Nasiru Awal MAB
January 4, 2018

An samu Mehmet Hakan Atilla da laifin karya ka'idojin takunkuman da Amirka ta sanya wa Iran. An zarge shi da taimaka wa Iran gudanar da kasuwanci na dubban miliyoyi ta barauniyar hanya.

https://p.dw.com/p/2qLNB
USA New York Prozess Goldhändler
Hoto: picture-alliance/AP Photo/E. Williams

Kasar Turkiyya ta yi tir da hukuncin da wata kotun a birnin New York na kasar Amirka ta yanke wa wani ma'aikacin bankin Turkiyya Mehmet Hakan Atilla tana mai kwatanta hukuncin da katsalande a cikin harkokinta na cikin gida.

A wani zaman shari'a da aka yi an samu Atilla da laifin karya ka'idojin takunkuman da Amirka ta kakaba wa Iran. Atilla da ke zama tsohon mataimakin shugaban bankin Turkiyya na Halkbank, an zarge shi da taimaka wa Iran gudanar da harkokin kasuwanci na miliyoyi dubbai ta haramtattun hanyoyi.

Masu taimaka wa alkali yanke hukunci a kotun ta tarayya da ke birnin New York sun samu manejan bankin da aika laifuka biyar daga cikin shida da wani mai ba da shaida kuma dillalin zinariya mai asali da kasashen Turkiyya da Iran ya yi zargi, ciki har da yi wa banki zamba da kuma yin makirci. Shi dai mutumin ya fada wa kotun cewa shugaban Turkiyya Tayyip Recep Erdogan na da masaniya kan batun kuma shi ya amince da harkar ta musayar gwal da man fetir.