1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiyya tayi watsi da shawarwarin Iraqi

October 27, 2007
https://p.dw.com/p/C15b

Turkiyya tayi watsi da shawarwarin da Iraqi ta gabatar,don yaki da yan tawayen kurdawa. A cewar Turkiyya wadannan shawarwari zasu dauki dogon lokaci, kafin su fara aiki a aikace. An jiyo ma´aikatar harkokin wajen ta Turkiyya na cewa, dole ne a dauki matakan gaggawa na dakile fitinar yan tawayen ta Kurdawa, a maimakon bin shawarwarin da Iraqi suka gabatar. A yanzu haka dai tawagar Iraqi na kasar ta Turkiyya don tattaunawa da mahukunta, bisa manufar samo bakin zaren wannan takaddama.Ziyarar dai tazo ne, a kokarin da Iraqi keyi na hana Turkiyya yin kutse izuwa cikin kasar tata ne da sunan yaki da tsagerun kurdawa. A yanzu haka dai akwai dubbannin dakarun sojin Turkiyya dake jibge a iyakar kasashen biyu, a matsayin shirin ko ta kwana, na afkawa yan tawayen na kurdawa.