1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Uganda: Cin hanci ya yi kamari a asibitoci

Salissou Boukari
September 16, 2017

Ministar kiwon lafiya ta kasar Uganda Sarah Opendi ta yi shigar burtu, inda ta kai kanta wani asibiti a matsayin maras lafiya, yayin da jami'an asibitin guda biyu suka sa ta biyan wasu kudade alhali kyauta ne.

https://p.dw.com/p/2k6dL
Uganda Krankenhaus Symbolbild
Hoto: AFP/Getty Images/I. Kasamani

Minista Sarah dai ta sanya hijabi ne inda ta hau Acaba ko kuma Kabu-kabu zuwa babban asibitin Naguru da ke Kampala babban birnin kasar a wani mataki na gane wa idanunta matsalar cin hanci da ke afkuwa a asibitin. Ministar kiwon lafiyar Sarah, ta ce ta sha samun kararraki daga jama'a kan ma'aikatan wannan asibiti, inda jami'an kiwon lafiyar ke tilasta wa jama'a biyan kudade kuma ta ce an tambaye ta ta biya Sule dubu 150 kwatankwacin Euro 35 domin a yi mata wasu gwaje-gwaje wadanda ya kamata a yi su kyauta.

Ministar ta ce daga bisani an tura ta wajen wata jami'ar jinya, inda ita ma ta nemi ta biya kudi. Nan take ministar ta kira 'yan sanda suka kama wadannan jami'an kiwon lafiyan biyu. Daga nashi bangare Darectan babban asibitin Stephen Kyebambe ya mika godiya ga Ministar da ta sa aka kama wadannan jami'ai. Cin hanci dai a gidajen asibitoci ya zama ruwan dare gama duniya a kasar Uganda da ma wasu kasashe da dama na Afirka.