1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

UN: Gargadi ga mahakuntan Jamus kan nuna kyama

Usman Shehu Usman
February 28, 2017

Kwararru na Majalisar Dinkin Duniya, sun yi hannunka mai sanda ga kasar Jamus, dangane da matsalolin da wasu 'yan kasashen Afirka ke fuskanta na wariya da cin zarafi.

https://p.dw.com/p/2YNqv
Deutschland Berlin Demonstration gegen Rassismus und Diskriminierung
Masu zanga-zangar nuna adawa da kyamar baki a JamusHoto: Reuters/S. Loos

Babban misali ga irin wannan wariya da bakaken fata daga Afirka ke fiskanta a kasar Jamus, shi ne abin da ya faru da Umar Jallo, wanda ya ga wariya a tashar jiragen sama na kasar Jamus, lokacin da ya dawo daga hutun da ya yi da buduruwarsa a kasar Spain.

"Ni ne kadai baki a cikin jirgin. Buduruwata wadda muka je hutun tare Bajamusa ce.  Ni ne kadai 'yan sandan suka tsare. Buduruwata ta yi matukar bata rai da lamarin. Ta tambayi 'yan sandan mi ya sa sai ni kadai za su bincika, sai 'yan sadan suka ce ki yi abinda zaki yi. Tsarewar da muka yi bata da alakar kasancewarsa bakar fata."

Nuna kyamar baki ba sabon abu ba ne a Jamus

Deutschland Demonstration 10. Todestag von Asylbewerber Oury Jalloh
'Yan sanda na kula da zanga-zangar adawa da nuna kyamar baki a JamusHoto: picture-alliance/dpa/J. Wolf

Ba Umar Jallo kadai ke bakar fatan Afirka da ke fiskantar irin wannan nuna wariya a kasar Jamus ba, kwarrun Majalisar Dinkin Duniya da ke kula da kare hakkin jama'a sun tattara alkaluma dayawa na irin wannan matsala, bayan bincike na kwanaki bakawai da suka yi a kasar ta Jamus. Ricardo Sunga, shi ne shugaba tawagar da ta zo Jamus.

"Daukacin rayuwar 'yan Afirka a Jamus ta kasance cikin nuna wariya, da bambanci a kusan duk al'amura da suke gudanarwa. Ana jefa musu kalaman nuna wariyar jinci da aikata manyan laifuka. 'Yan Afirka na cike da tsoro ko wane lokacin don gudun kada a farmusu, har ta kai ba sa shiga wasu wuraren don gudun farmaki. Suna cikin kyama da wariya daga abokan aiki ko na karatu, ko daga malamansu a makarantu. Uwa-Uba akwai tsarin gwamnati da aka yi bisa manufar nuna wariya, haka ma dokokin kotunan kasar."

Majalisar Dinkin Duniya ta yi tir da nuna kyama

New York City Außenminister Gabriel in den USA mit Guterres Un Generalsekretär
Ministan harkokin wajen Jamus tare da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Hoto: picture-alliance/dpa/B. von Jutrczenka

A ziyarar bincike da hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya ta kawo a Jamus, kwararrun sun gana da 'yan majalisar dokoki da mukarraban gwamnati, da ma wasu wakilan kasashe kana da kungiyoyi masu zaman kansu da ke da alaka da Afirka. Karen Taylor wadda iyayenta 'yan asalin kasar Ghana ne, ta kafa wata kungiya mai fafitikar kare yancin bakaken fata a Jamus.

"Nuna kyama ga 'yan Afirka kuskure ne, kamata ya yi kowa ya je Afirka ya gani da idonsa rauywar Afirka, kafin ya yanke hukunci kan mutanen Afirka. A wurare da yawa ake nuna bambanci, misali in baka jin Jamusanci ko daukanka aiki baza'a yi ba, haka wajen neman dakin haya idan kai dan Afirka ne, to sai an rasa wanda za a bai wa sannan ka samu, wadannan matsaloli ne a kullun muke fiskanta"

Binciken hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya mai kula da kare hakin jama'a, ya gano cewa kashi 63 cikin 100 na Jamusawa su na dauke da ra'ayin nuna wariyar jinsi, inda wasunsu ke yin haka don kare lafiyarsu. Sai dai Majalisar Dinkin Duniya ta buka ci a kawo sauyi kan lamarin, wanda kuma ana bukatar yin kwaskwarima ga dokokin aikin 'yan sandan Jamus. Domin bai wa masu korofi damar kawo kukansu. kafin yanzu dai wadanda ke da korofi kan irin wadannan matsaloli ba su da damar yin hakan.