1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Venezuela ta gargadi Amirka kan harkokin siyasa

Ibrahim SaniDecember 1, 2007
https://p.dw.com/p/CVQm

Shugaba Hugo Chavez na Venezuela ya gargadi Amirka da daina katsalandan, a harkokin siyasa a ƙasar. Gargadin ya zo ne kwana ɗaya a gudanar da zaɓen raba gardama, a game da ƙoƙarin yiwa kundin tsarin mulkin ƙasar kwaskwarima. Goyon bayan da Amirka ke ba wa ´Yan adawa na ƙasar a cewar Mr Chavez, abune da ka iya gurgunta zaɓen da ake shirin gudanarwa a gobe lahadi. Mr Chavez ya kara da cewa Venezuela a shirya take ta mayar da martani ga Amirka ta hanyar katse man da take bawa ƙasar. Batun kawo ƙarshen wa´adin shugaban ƙasa da kuma cikakken ikon shugaban babban bankin ƙasar na daga cikin abubuwan da za a yiwa kwaskwarima, a cikin kundin tsarin mulkin ƙasar. Hakan dai a cewar masu nazarin siyasa, ka iya bawa shugaban damar yin ta zarce a karo na uku a jere.