1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

wa ya kirkiro Danjar-kan titi

Abba BashirMay 8, 2006

bayani akan samuwar Danjar-kan titi

https://p.dw.com/p/BvVT
Danjar-titi
Danjar-titiHoto: AP

Jama’a masu sauraronmu assalamu alaikum, barkammu da wannan lokaci, barkammu kuma da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na amsoshin takardunku,shirin da yake amsa tambayoyin da ku masu sauraro kukan aikomana.

Tambaya:Fatawarmu ta wannan makon ta fito daga hannun Malama Maryam Jafaru , Tunis-Belvedare, a can Kasar Tunisiya. Malamar ta ce , shin wane mutum ne ya kirkiro da Danjar kan-titi mai ba da hannu, wadda aka fi sani da “Traffic lights’’ a Turance?

Amsa: To “Traffic Lights’’ ta farko a Duniya dai wata fitilar kwai ce mai amfani da iskar gas wadda take da haske iri biyu wato Ja da kuma Kore,kuma an maiala ta ne a Birnin London a wata Mararraba da ake kira “Lodon Intersection’’ a Turance, a shekarar 1868, wannan kuwa ya faru tun kafin a kirkiro fasahar kera motoci.Daga baya an sake kirkirar wani samfuri irin na waccan fitilar domin amfani da ita a titunan Jiragen-kasa a Birnin Detroit, Michigan a shekara 1920. To amma wanda ya samo fasahar yin Danjar-titi irin ta zamani da ake gani a halin yanzu, wani Mutum ne wai shi Garrett Augustus Morgan.

Shi dai Mr Augustus Morgan Da ne daga cikin “Yayan tsofaffin bayi bakaken fata na Kasar Amurka,kuma an haifeshi ne a shekarar 1877 a garin Kentucky,daga baya kuma ya koma garin Cincinnati, inda daga nan kuma yayi kaura zuwa garin Cleveland da zama .

Tun a farkon Krni na 20. Birnin Celevland kamar sauran manyan biranen Amurka , hanyoyin sa sun cushe sakamakon cunkoson Mutane masu tafiya a kasa da masu kekuna da kekunan dabbobi,kamar su keken-doki ko keken-shanu da dai sauran Abubuwan hawa na wancan lokaci. Kuma a waccan lokaci babu wata dokar ba-da-hannu a kan tituna , saboda haka a kullum cunkoso sai kara tsananta yake yi, kuma hadurra suna faruwa akai-akai. To sakamakon wani hadari da aka yi akan idon shi Mr Morgan , sai ya ga cewar ya zama wajibi akan sa ya samar wa da Al’umma mafita ta wannan garari da suke ciki, saka makon haka shine ya haifar da kirkirar irin wannan danjar kan titi ta zamani a ranar 23-11-1923.

To sai dai bakamar danja irin wadda ake gani a halin yanzu ba , danjar kan titi wadda Mr Morgan ya kirkiro ya yi ta ne a siffar gwafa, inda take bada umarni ta bangarori guda uku, wato tsayawa,tafiya dakuma tsayawa ta kowanne bangaare. Wannan tsayawa ta kowanne bangare na nufin duk wani abin hawa ya tsaya domin masu tafiya a kasa su sami damar tsallaka titi lami lafiya.wannan samfurin danjar tituna dai ta Mr Morgan, ita ce ake amfani da ita gaba dayan Yankin Amurka ta Arewa,kafin a maye gurbinta da irin wadda ake gani ta zamani a halin yanzu ,wato Ja/Rawaya/Kore.