1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wai takardar da shugaba Ahmadinijad ya aike wa shugaba Bush ba ta da muhimmanci kuwa ?

YAHAYA AHMEDMay 9, 2006

Kafin taron ministocin ƙasashe masu kujerun dindindin a kwamitin na Majalisar Ɗinikin Duniya ne shugaba Ahmadinijad na ƙasar Iran ya aike wa takwaran aikinsa na Amirka George W. Bush, wata takarda mai shafi 18, wadda ba a bayyana abin da take ƙunshe da shi ba takamaimai. Ita Amirkan dai ta ce takardar ba ta ɗauke da komai illa kame-kame. Wai shin hakan ne kuwa ?

https://p.dw.com/p/Bu0F
Ahmedinijad da George W. Bush
Ahmedinijad da George W. BushHoto: AP

Ba a dai bayyana saƙon da takardar da shugaba Ahmadinijad na ƙasar Jumhuriyar Islama ta Iran ya aike wa takwarar aikinsa na Amirka, George W. Bush, ke ɗauke da shi ba. Sai dai, a birnin Washington, bayan karanta wasiƙar mai shafi 18 da aka yi, fadar White House ta bayyana cewa babu wani sahihin abin da ta ƙunsa, illa kame-kame.

Wannan yanayin sirrin da aka ƙago a kewayen takardar dai wato abin ban takaici ne. Da ya kamata a bayyana duk abin da da take ɗauke da shi don duk duniya ta yanke tata shawarar. Har ila yau kuma, takarda daga shugaban Iran zuwa ga takwaran aikinsa na Amirka, ai wani sabon abu ne da ya kamata a ba shi muhimmanci, ko da ana zaton cewa, wato wata dabara ce da Iran ɗin ta saba yi, don rarraba hankullan jami’an diplomasiyya har a gaza cim ma daidaito kan zartad da ƙuduri a kanta a kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya. Ala kulli halin, ko da wannan takardar ko da rashinta, an dai yi taron ministocin harkokin wajen ƙasashe masu kujerun dindindin a kwamitin sulhun da kuma na Jamus. Sai dai, ban da cin abincin da aka daɗe ana yi, babu wani muhimmin sakamakon da aka cim ma, abin da ke nuna cewa, har ila yau dai, mahalarta taron sun gaza samun ra’ayi na bai ɗaya wajen zartad da ƙudurin kan Iran.

A shekaru 25 da suka wuce, yayin da Isra’ila ta kai harin bam kan wata cibiyar makamashin nukiliyan da Iraqi ta giana a Osirak kusa da birnin Bagadaza, Majalisar Ɗinkin Duniya ta zartad da ƙuduri mai lamba ɗari 4 da 87, inda ta yi Allah wadai da wannan matakin da ƙasar Bani Yahudun ta ɗauka. A wannan lokacin dai, Isra’ila ta hujjanta kai harin ne da yin matashiya da kundin ƙa’idodjin Majlisar mai lamba 51, wadda ke bai wa ko wace ƙasa damar kare kanta idan an yi mata barazana ko kuma an kai mata hari. Amma Majalisar ta yi watsi da hujjar, tare kuma da bai wa Iraqi damar gudanad da binciken nukiliya ta hannunka mai sanda. Kazalika kuma, ta bukaci Isra’ilan da ta sanya hannu kan yarjejeniyar nan ta hana yaɗuwar makakaman nukiliya, ta kuma biya diyya ga Iraqi, saboda asarar da ta janyo mata sakamakon wannan harin.

A yanzu dai bisa dukkan alamu, Washington ta manta da wannan ƙundurin da aka zartar a Majalisar Ɗinkin Duniya. Idan kuma za a tuna, a daidai wannan lokacin ne, aka sami hauhawar tsamari matuƙa, tsakanin ƙasashen Yamma da sabuwar Jumhuriyar Islama ta Iran. A yamman dai ana fargabar ganin kafuwar gwamnatin sabuwar Jumhuriyar ta Islama a birnin Teheran. Sabili da haka ne aka yi ta bai wa Saddan Hussein goyon baya, a yaƙin da yake yi da Iran ɗin. Kai har Faransa ce ma ta sake gina wa Iraqin tashar nukiliyan da Isra’ila ta ragargaza da bamabamai. Ƙudurin Majalisar Ɗinkin Duniya da aka zartar kan Isra’ila a wannan lokacin, ba kan adalci aka zartad da shi ba. Ƙasashen Yamma, ƙarƙashin jagorancin Amirka, sun goyi bayan ƙudurin ne saboda matuƙar adawar da suke yi da juyin juya halin da aka yi a Iran, da kuma mara wa Saddam Hussein bayan da suke yi.

To ga shi dai yau shekaru 25 da suka wuce, Saddam Hussein da aka yi ta nuna wa goyon baya, na ɗaure a kurkuku, yana huskantar shari’a a birnin Bagadaza. Zargin da ake yi wa Iran a yanzu kuma, shi ne wanda aka ƙi yi wa Iraqi a wancan lokacin. Ashe ko ba abin mamaki ba ne da yanzu ɗin, Rasha da Sin ke nuna matuƙar adawa ga zartad da ƙuduri kan Iran, saboda su ma suna sha’awar kare maslaharsu ta tattalin arziki a ƙasar Jumhuriyar Islaman.

Bisa raɗe-raɗi dai, akwai kyawawan shawarwari da ke ƙunshe cikin takardar da shugaba Amadinijad ya aike wa shugaba Bush, waɗanda ke nufin inganta hulɗodi tsakanin ƙasashen biyu. Idan da ɗumi-ɗumin gaskiya a wannan batun, to ai kuwa da ya dace Amirka ta sake nazarin takardar, ba kawai ta yi watsi da ita tamkar wata tsumma ba.