1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wakilin Majalisar Dinkin Dunia a gabas ta tsakiya ya bayana damuwa a kan halin da yankin ke ciki

July 4, 2006
https://p.dw.com/p/Burb

Wakilin Majalisar Ɗinkin Dunia a yankin gabas ta tsakiya, ya bayana damuwa, a game da tabarbarewar zaman lahia tsakanin Isra´ila da Palestinu, bayan sace sojan Isra´ila da wasu dakarun sari ka noƙen Palestinawa su ka yi.

Alvarato de Soto, ya ce ko kamin faruwar al´amarin yankin gabas ta tsakiya ya kasance gurbatace, to amma a halin da ake ciki, tashin hankalin ya kai intaha.

A yunkurin da ta ke na gano sojan ta ta ko wane hali, Isra´ila na ci gaba da kai hare ahren a zirinGaza, tare da jawo assara mai tarin yawa.

Ranar 28 ga watan da ya gabata, rundunar Isra´ila ta tarwatsa wata cibiyar samar da wutar lantarki,a zirin Gaza.

A sakamakon haka, mazauna yankin, sun faɗa cikin matsanancin hali ,na rashin tsabtattun ruwan sha,da kuma karancin wutar lantarki.

Bugu da ƙari cuttutuka iri-iri sai ƙara yaɗuwa su ke.

Alvaro de Soto ya bayyana adawar Majalisar Ɗinkin Dunia, a game da matakin da gwamnatin Isra´ila ta ɗauka, na capke ministoci da kuma yan majalisun dokokin Hamas.