1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wane ne ya ƙirƙiro da na'urar sanyaya ɗaki

June 16, 2009

Taƙaitaccen tarihin yadda aka samar da na'urar sanyaya ɗaki

https://p.dw.com/p/I5Lh
Yanayin zafi ke nan.Hoto: picture-alliance/dpa

Tambaya: Fatawarmu ta wannan makon ta fito daga hannun malam Ya'u Bala Abubakar daga ƙasar Ghana. Ya ce, DW ku ba ni tarihin mutumin da ya ƙirƙiro da na'urar sanyaya ɗaki, wadda Bature ke kira 'air conditioner'.

Amsa: Duk da cewa dai na'urar sanyaya wuri wato 'air conditioner', ba wai kawai a gidaje ake samun ta ba, har ma a na'urorin nasara, irin su motoci da jirage dadai sauran su. To ita dai na'urar sanyaya waje kamar sauran kere-kere na kimiyya da fasaha, za a ga cewa, ba wai aikin wani mutum ne shi kaɗai ba. Aiki ne na mutane da dama, a mafi yawan lokuta ma za'a tarar cewa, wanda ya fara gano fasahar daban, wanda kuma ya ƙera na'urar daban. To haka ma abin yake ga sha'anin ƙera na'urar sanyaya wuri.

To bari mu fara da mutumin da ya fara ƙago fasahar samar da na'urar sanyayyawa, wanda shi ne fitaccen masanin kimiyyar nan mai yawan ƙirƙire-ƙirƙire a ƙarni na 19 wato, Michael Faraday. Shi ne mutumin da ya fara gano fasahar da za a iya tattara iska a danƙare ta waje guda a cikin wani bututu ko kuttu, sai kuma a samar da wata 'yar kafa da za ta ba da dama ga wani sinadari da ke cikin iskar wanda ake kira 'amoniya', ya riƙa tashi, to hakan zai sa a samu sanyayyar iska. To sai dai wannan hikima ta Faraday a rubuce kawai ya bar ta, ba a gwada ta a aikace ba.

To a shekarar 1842, sai wani masanin kimiyyar ɗan jihar Florida ta ƙasar Amirka da ake kira da suna Dr. John Gorrie, ya yi amfani da waccan fasaha ta Michael Faraday ya ƙago yadda za a iya yin ƙanƙara. Kuma ya yi haka ne da nufin samar da wata na'ura da za ta riƙa sanyaya jikin masu fama da raɗaɗin zazzaɓin cizon sauro da na jante ko 'yar lisuwa. An ma ce, kafin ya rasu yana da burin samar da na'urar da za ta sanyaya gabakiɗayan gari ba ma wani gida guda ɗaya ba, to amma dai ita na'urar tasa ƙanƙara kawai take samarwa.

Tun daga wancan lokaci ba a sake tayar da batun na'urar sanyayawa ba sai a shekarar 1902, shekara ɗaya bayan da wani masanin kimiyya da fasaha da ake kira Willis Haviland Carrier, ya kammala digirinsa na uku a hakar fasahar ƙere-ƙere, daga jami'ar Cornell, da ke birnin New York a ƙasar Amirka, a wannan lokaci ne aka samar da na'uwar sanyaya ɗaki ta farko wadda take fitar da iska mai sanyi haɗe da raɓa. Willis Haviland ya gano wannan ne a shekarar da wani kamfanin buga litattafai da mujallu da ake kira da suna Buffalo Forge Company, ya ɗauke shi aiki.

Kafin a ɗauki Havilanda aiki, wannan kamfani suna samun matsala da injinansu, inda wani lokaci injinan sukan birkita rubutu ko kuma su hatgitsa kalolin idan ana cikin yin ɗab'i. Saboda tsananin zafin da suke ɗauka idan aiki yai aiki, Amma bayan da Haviland ya ƙera na'urar sanyaya ɗaki sai komai ya tafi daidai. Inda akai ta godewa sabon ma'aikacin da aka ɗauka a Buffalo Forge Company, wanda kuma alokacin albashinsa ya fara ne da dala $10.00 kacal a kowanne sati.

Likkafa ta ci gaba a wajen Havilanda bayan da aka ba shi lambar ƙira, ta mallakar fasahar ƙera na'urar sanyaya ɗaki. Inda daga baya ya rubuta dabarar da ya yi amfani da ita wajen ƙera wannan na'ura, wadda kuma wannan dabara ita ce har yanzu masana ilimin fasahar ƙere-ƙere na wannan zamani suke amfani da ita wajen ƙera nau'o'i daban-daban na na'urorin sanyayyawa, ko dai sanyaya gida ko masana'anta ko ofis ko mota ko jirgi da dai sauransu.

Mawallafi: Abba Bashir

Edita: Yahouza Sadissou Madobi