1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wane shugaban ƙasa ne mafi ƙarancin shekaru a duniya

Bashir, AbbaMarch 12, 2008

Bayani game da shugaban ƙasar da ya fi dukkanin shugabannin ƙasashen duniya ƙarancin shekaru

https://p.dw.com/p/DNdV
Shugaban Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo Joseph KabilaHoto: AP

Masu saurarommu assalamu alaikum, barkammu da wannan lokaci, barkanmu kuma da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na Amsoshin takardunku, shirin da a kowane mako yake amsa wasu daga cikin tambayoyin da kuka aiko mana.

Tambaya: Wai shin wane shugaban ƙasa ne ya fi ƙarancin shekaru a tsakanin shugabanin ƙasashen duniya, kuma ku sanar da ni shekarun sa nawa ne a halin yanzu, sa'annan ku ba ni taƙaitaccen tarihin sa? Wannan ita ce tambayar Mardhiyya Abdul'aziz, daga birnin Umdurman na ƙasar Sudan.

Amsa: Shugaban jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo, Joseph Kabila, shi ne shugaban ƙasa da ya fi ƙarancin shekaru a tsakanin shugabanin ƙasashen duniya. Joseph Kabila, ya hau mulki ne bayan mutuwar mahaifinsa, Laurent D. Kabila tsohon shugaban ‘yan tawayen Congo, wanda dogarawansa suka kashe shi a watan Janairu na shekara ta 2001. Bayan mutuwarsa da kwanaki goma, aka zaɓi ɗansa Joseph Kabila a matsayin shugaban Jamhoriyar Dimokuraɗiyyar Congo.

Joseph Kabila shugaban Jamhoriyar Dimokuraɗiyyar Congo an haife shi ne a ranar 4, ga watan yuni, na shekarar 1971. Yau shekarunsa 37, kenan da haihuwa, kuma duka-duka bai shige shekaru 30 da haihuwa ba ya zama shugaban Congo.

Joseph Kabila shine babban ɗan shugaba Lawrent Kabila, daga cikin 'ya'yansa goma. Joseph Kabila ya zama zaɓaɓɓen shugaban Congo a shekara ta 2006.

Gwamnatocin ƙasashen yammacin duniya kamar su Amirka da Faransa, tare da wasu gwamnatocin ƙasashen Afirka da suka haɗa da Afirka ta kudu, da Angola, sun yaba tare da bayyana goyon bayan su ga zaɓen Jospeh Kabila a matsayin shugaban Congo, musamman yadda suka cimma moriyar wasu harkoki na kasuwanci na miliyoyin dala, a zamanin gwamnatinsa.

Shugaban na Congo, wanda ya sami horonsa na aikin soji daga ƙasar Sin, ya kasance dumu-dumu cikin ‘yan yaƙin sari ka noƙe a zamanin da ƙasar ta sha fama da yaƙe-yaƙe. Joseph Kabila ya taimaka wa mahaifinsa, wajen kifar da gwamnatin Mobutu Sese Seko, a shekarar 1997, bayan da gwamnatin Mobuto na Zaire a wancan zamani ta shafe shekaru fiye da 20, tana shugabanci.