1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wanene Dan-ta'adda

Abba BashirFebruary 13, 2007

Dangantakar Ta'addanci da Gabas ta tsakiya

https://p.dw.com/p/BvUy
Gini yana cin wuta
Gini yana cin wutaHoto: AP

Mutanen da suke cewa suna aiki da sunan addini na iya rashin fahimtar addininsu ko su aikata shi abisa kuskure. Saboda haka, kuskure ne samo wani abu daga wurin wadannan mutanen akan abinda ya shafi addini. Hanya mafi kyawun fahimtar addinin Musulunchi shine ta asali mafi tsarki.

Hanya mafi tsarki a Musulunchi shine Alkur`ani: kuma samfurin kyawawan dabi`u kur`ani shine Musulunchi-ya sha bamban da duk wani yanayin da ya darsu a zukatan wasu turawan yamma. An saukar da kur`ani ne akan kyawawan dabi`u, soyayya, tausayi, jinkai, kaskantar da kai, kwazo, juriya da zaman lafiya, kuma Musulmin da yake rayuwa akan wannan tafarki, lallai ya tsarkaku, ga hangen nesa, juriya, gaskiya da rikon amana. Wadanda suke kewaye dashi na amun kauna, girmamawa, zaman lafiya da fahimtar zaman takewa ta rayuwa tare dashi.


Musulunchi addinin zaman lafiya ne da kwanciyar hankali

Kalmar ISLAM tana daidai da ma`anar "zaman lafiya" a larabce. Musulunchi saukakken addini ne da ya zowa rayuwar dan Adam cike da zaman lafiya da kwanciyar arziki, wanda rahama da jinkan Ubangiji ya bayyana a duniya. Ubangiji yayi kira ga mutane suyi koyi da kyawawan dabi`un da kur`ani ya koyar a matsayin abin koyi daga rahama, jinkai, juriya da zaman lafiya wanda duniya za ta dandana. A suratul Baqara, aya ta 208, an bada wannan umarni kamar haka;

" Yaku wadanda suka yi imani! Ku shiga cikin Musulunchi gaba daya;kuma kada ku bi zambiyoyin Shaidan;lalle ne shi a gareku makiyi ne, bayyananne. "

Kamar yadda muka gani a wannan aya, mutane zasu iya samun rayuwa mai walwala kadai idan sun shiga Musulunchi kuma suka rayu akan koyarwar Alkur`ani.

Allah ya hana zalunci

Ubangiji ya umarci dan Adam da ya guji barna, kafirci, rashin mutunci, kangarewa, kisan kai, da zubar da jini. Wadanda suka sabawa wannan umarni to lallai suna kan tafarkin Shaidan, kamar yadda aka bayyana a ayarda ta gabata, kuma aka bayyana shi da cewa abin haramtawa ne daga wurin Ubangiji. Daga cikin ayoyi masu yawa da suka yi bayani akan haka, ga guda biyu;

"wadanda suka warware alkawarin Allah daga bayan kulla shi, kumasuna yanke abinda Allah yayi umarni dashi domin a sadar dashi kuma suna barna a cikin kasa. Wadancan suna da wata la`ana, kuma suna da munin gida. "(suratul ra`ad:aya ta 25)

"A Kuma ka nema, a cikin abinda Allah ya baka gidan lahira, kuma kada ka manta da rabonka daga duniya. Kuma ka kyautata kamar yadda Allah ya kyautata zuwa gareka, kada ka nemi barna a cikin kasa. lalle ne Allah ba ya son barna"(suratul qasas:aya ta 77)

Kamar yadda zamu iya gani, Ubagiji yayi hani ga duk wani nau`i na zalunci a addinin musulunchi, har da ta`addanci da hada tarzoma, kuma ya la`anci masu aikata hakan. Musulmi shine zai iya arawa duniya kyau ya kuma ingantata.


Musulunchi Na kare Iko da `yancin Magana.

Musulunchi addini ne da yake tabbatar da `yancin rayuwa, fahimta da tunani. Yayi hani ga tashin hankali, rigingimu, rudani, da zato kai har da mugun tunani da ka iya yiwa wani illa. Musulunchi ba wai kawai ya hana ta`addanci ko tarzoma ba, kai duk kankantar abinda zai iya cutarwa akan wani dan Adam an hana shi.

"Babu tilastawa a cikin addini, hakika shiriya ta bayyana daga bata; saboda haka wanda ya kafirta da Daguta kuma yayi imani da Allah, to, hakika yayi riko ga igiya amintacciya, babu yankewa a gareta. Kuma Allah mai ji ne, masani. "(Suratul baqara: aya ta 256).

"Ka isar musu da gargadi, domin gargadi ne kawai gareka, baka da ikon tursasa su akan suyi imani. "(Suratul ghashiya: 22)

Tilastawa mutum yayi imani da addini ko aikatashi, ya sabawa hikima da manufar musulunchi saboda wajibi ne ace imani ya karbu ta hanyar sakakkiyar iko da zabin zuciya. Koda yake, musulmi ya iya kwadaitar da wani akan bin koyarwar Alkur`ani, amma ba tare da tilastawa ba. Haka kuma, ba `a son jan hankalin mutum izuwa addini ta hanyar bashi wani abin amfani na duniya.

Amma bari mu kwatanta abin a kishiyance. Misali, kasar da ake matsawa mutane da dokar kasa don su yi addini. Wannan kasa ko al`umma ta sabawa addinin musulunchi saboda imani da bauta suna kima idan har an fuskantar dasu ga Allah. Idan dai har akwai wani tsari dake tilastawa mutane su yi imani da bauta, to mutane zasu zama suna biyayya ne don tsoron wannan tsari kawai. Abinda yake karbabbe ta fuskar addini shine, addini yana aiwatuwa ne a cikin al`ummar da take da `yancin rayuwa, kuma a aikata shi da nufin yardar Ubangiji.


Allah ya haramta kisan mutanen da basu ji ba , basu gani ba

. Kamar yadda Alkur`ani ya bayyana, daya daga cikin manyan zunubai shine kashe mutumin da bai yi wani laifi ba.

"Daga sababin wannan, Muka rubuta akan Bani Isra`ila cewa, lalle ne wanda ya kashe rai ba da wani rai ba, ko barna a cikin kasa, to kamar ya kashe mutane duka ne, kuma wanda ya raya rai, to, kamar ya rayar da mutane ne gaba daya. Kuma lalle ne, hakika, ManzanninMu sunje musu da hujjoji bayyanannu, sannan kuma lalle ne, masu yawa daga gare su, a bayan wannan, hakika, masu barna ne a cikin kasa. "(suratul ma`ida:aya ta 32);

"kuma wadanda ba su kiran wani Ubangiji tare da Allah, kuma ba su kashe rai wanda Allah Ya haramta face da hakki, kuma wanda ya aikata wancan, zai gamu da laifuffuka. "(suratul furqan:aya ta 68).

Kamar yadda muka gani a wadannan ayoyi na sama, wadanda suka kashe mutanen da ba su jiba ba su gani ba, to ana tsoratar dasu da azaba mai radadi. Ubangiji ya bayyana cewa kashe mutum, girmansa kamar kashe mutane ne baki dayansu. Duk wanda yake girmama dokokin Allah ba zai cutar da wani ba, ballantana yayi sanadiyyar kashe miliyoyin mutanen da basu jiba basu gani ba. Wadanda suke tunanin kubuta daga hukunci anan duniya, ba zasu taba kubuta daga tambayar da zasu amsa a gaban Ubangiji gobe kiyama ba. Saboda haka, mummunan da suka san cewar zasu bada bayani gaban mahalicci bayan mutuwarsu, zasu yi taka-tsantsan wajen kula da dokokin da Ubangiji ya shimfida.


Allah Ya Umarci Mummunai da su Zama Masu Rahama da Jinkai.

A wannan aya, an bayyana dabi`un musulmi da cewa;

"Sannan kuma ya kasance daga wadanda suka yi imani, kuma suka yiwa juna wasiyya da yin hakuri, kuma suka yiwa juna wasiyya da tausayi. Wadannan ne ma`abota albarka. "(suratul balad:aya ta 17-18).

Kamar yadda muka gani a wannan aya, daya daga cikin abubuwa masu muhimmanci a kyawawan dabi`un da Ubangiji ya saukarwa bayinsa ko sun samu gafara da jinkai da samun aljanna shine su "kwadaitar da junansu da yin rahama."

Kamar yadda Alkur`ani ya siffanta musulunci da cewa addini ne na kowane zamani, mai wayar da kai da samar da cigaba. Musulmi shine wanda yafi kowa son zaman lafiya, mai iya juriya da yanayin zamantakewar siyasa, mai riko da al`adun addini, mai gaskiya kuma wayayye, masani akan rayuwa, kimiyya da wayewar zamani.

Musulmi masani ne ga kyawawan dabi`un da alkur`ani ya koyar, yana mu`amala da kowa tare da soyayya irin wadda musulmi yake bukata. Yana girmama dukkan wata hikima, kuma yana kimanta ilmi. Kuma shi mai kawo sulhu ko hadin kai ta kowace fuska, tare da kawar da duk wani rikici ko sabani. A cikin al`ummar da ake samun irin wadannan mutane, za`a samu cigaban rayuwa, farin ciki da walwala, adalci, tsaro, yawan albarka fiye da kowace kasa mai cigaba a wannan duniya ta yau.


Ubangiji Ya Umarci Kawaici da Gafara

Suratul A`raf, aya ta 199, wadda tace "ku yawaita gafara", na nuna cewar kawaici da gafara suna daya daga cikin ginshikan addinin musulunci.

Idan muka kalli tarihin musulunci, zamu gani a bayyane yadda musulmi suka kafa wadannan muhimman dabi`u daga koyarwar alkur`ani a rayuwarsu ta yau da kullum. A kowane lokaci a rayuwarsu, musulmi sun rushe dukkanin haramtattun ayyuka kuma sun tabbatar da zaman lafiya. A bangaren da ya shafi addini, harshe da al`adu, sun saukaka rayuwa inda mabanbantan mutane suka rayu a inuwar `yanci da zaman lafiya, kuma suka bawa wadanda suke karkashinsu damar yin ilmi, tara dukiya da samun matsayi na shugabanci. Wannan yana daya daga muhimman dalilan da ya fadada daular Ottoman kuma ta dade karnuka masu yawa, domin wannan shine tsarin rayuwartìyawa, kuma su samu damar walwalar rayuwa da al`adunsu ba tare da wani tsangwama ba.

Hakika, kawaicin musulmi, idan aka aiwatar kamar yadda Alkur`ani yayi umarni, zai kawowa duniya zaman lafiya da karuwar arziki. Alkur`ani ya bayyana irin wannan dabi`a da cewa;

" Kuma kyautatawa bata daidaita da munanawa. Ka tun kude da yake mafi kyau, sai gashi wanda akwai kiyayya a tsakaninka da tsakaninsa, kamar dai shi majibincin ne masoyi. "(suratul fussilat: aya ta 34)


Kammalawa

Dukkanin wadannan suna nuna kyawawan dabi`un da addinin musulunchi ya gabatarwa dan Adam a matsayin abinda zai kawo zaman lafiya, farin ciki da adalci ga duniya. Abubuwan da suke faruwa na rashin jin dadi a duniyarmu ta yau a karkashin sunan addinin musulunci, "Ta`addanci", ya fita daga tsarin koyarwar Alkur'ani, aiki ne na jahilai, mutane masu ketare iyaka, masu laifi wadanda ba ruwansu da addini. Hanyar da za'a yaki wadannan mutane da suke fakewa da musulunci, shine umartar mutane don suyi aiki da hakikanin koyarwar addinin musulunci.

A takaice dai, addinin musulunci da koyarwar Alkur'ani basa goyon bayan ta'addanci da 'yan ta'adda sai dai suna kawo hanyar da duniya zata kubuta daga ta'addanci.