1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wani dan bindiga ya halaka mutane a Amirka

Lateefa Mustapha Ja'afarJune 12, 2016

Akalla mutane 50 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu sama da 40 suka jikata sakamakon wani hari da aka kai a wata mashaya a birnin Orlando na jihar Florida.

https://p.dw.com/p/1J5Dv
Jami'an tsaron Amirka a Florida
Jami'an tsaron Amirka a FloridaHoto: picture-alliance/AP Photo/P. M. Ebenhack

Rahotanni sun nunar da cewa kawo yanzu an gazaya da mutane 42 da suka jikata sakamakon harin da aka kai a mashayar Orlando da ke Floridan zuwa asibiti. Jami'an 'yan sandan Amirka sun sanar da cewa mutane da dama sun rasa rayukan nasu bayan da tawagar jami'an tsaro ta isa mashayar, da nufin tseratar da mutanen da wani dan bindiga ya yi garkuwa da su a ciki.

Sai dai 'yan sandan sun sanar da cewa babu wata alaka tsakanin harbe-harben na wannan Lahadin, da kuma harbin da aka yi wa wata fitacciyar mawakiya a Amirkan cikin mako mai karewa, wanda kuma ya yi sanadiyyar mutuwarta. Sai dai a hannu guda hukumar leken asirin Amirka ta FBI ta ce ta yi wu maharin na da alaka da masu kaifin kishin addini.