1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wani hari a Sri Lanka ya halaka mutane da yawa

January 16, 2008
https://p.dw.com/p/CqFs

Hukumomin ƙasar Sri Lanka sun ce aƙalla mutane 26 sun mutu sannan wasu 70 sun jikata a wani harin bam da aka kai kan wata bas dake cike da mutane. Da yawa daga cikin waɗanda harin ya rutsa da su yaran makaranta ne. An kai harin ne a yankin Buttala mai tazarar kilomita 200 kudu maso gabashin Kolombo babban birnin ƙasar. Ana zargin ´yan tawayen kungiyar Tamil Tigers da hannu a wannan aika-aika. A yau laraba a hukumance shirin tsagaita wuta na shekaru 6 tsakanin gwamnati da ´yan tawayen yake karewa. Saboda ƙaruwar hare-hare da ´yan tawayen suke kaiwa, kimanin makonni biyu da suka wuce gwamnatin kasar ta ba da sanarwar janyewa daga yarjejeniyar tsagaita wutar wadda kasar Norway ta shiga tsakani aka kulla.