1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wani jirgin ruwa na yaƙi na Korea ta arewa ya tarwatse cikin teku

March 26, 2010

Ta'adama na shirin ɓarkewa tsakanin Ƙorea ta Arewa da ta Ƙudu

https://p.dw.com/p/MfUG
Jirgin ruwan Koriya ta KuduHoto: AP

 Wani jirgin ruwa na yaƙi na korea ta ƙudu ya tarwatse a cikin ruwan teku a kusa da kan iyaka da Korea ta arewa bayan da wani abu da har yanzu ba a san ko minene ba ya fashe a cikin Ahalin da ake ciki dai rahotanin sun nuna cewa masu aikin agaji sun yi kokarin ceto mutane 58 cikin mutun 104 dake cikin jirgin,yanzu haka dai gwamnatin ta Koreya ta ƙudu ta kira taron gaugawa akan wannan al amari.kanfanin dilanci labarai na kasar korea ta ƙudu Yonhap ya ce jirgin na koreya da farko ya ɓude wuta ne akan wani abin da ke a gabansa da bai tantance ko minene ba,to amma kuma daga bisani an ambato kakakin gwamnatin ya na mai cewa abinda jirgin ya harbi tsuntsya ne da suka tashi.wani babban jami 'i daga fadar gwamnatin ta Korea ta Ƙudu Kim Hye ya ce ba mamaki makobtiyar kasar wato Koreya ta Arewa ta na da hannu a cikin wannan aiki na asha  

Mawallafi :Abdourahamane Hassane

Edita : Abdulahi Tanko Bala