1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wani jirgin sama na ƙasar Indiya ya yi haɗari

May 22, 2010

Mutane a ƙalla 160 suka mutu a cikin wani haɗarin jirgin sama a ƙasar Indiya

https://p.dw.com/p/NUgc
Wani jirgin saman mallakar Air IndiyaHoto: dpa

  A ƙalla mutane 160 suka mutu a cikin wani haɗarin jirgin sama da ya auku a kuɗancin ƙasar Indiya .Jirgin samfarin Boeing 737 na kamfanin Air indiya,  wanda ya taso daga Dubai ɗauke da mutane 166, ya tarwatse ya yi  ɗaya ɗaya bayan da ya kama da wuta,a sa'ilin dake kokarin sauka  ya kuma  zarce, daga kan hanyarsa.kilomita ɗaya kafin filin saukar jiragen sama na Mangalore wanda ke a yammacin Bangalore hed kwatar Karnataka.

yanzu  haka dai wasu rahotanin dake zuwa da ke karo da juna na nuna cewa babu wani wanda ya tsira da ransa a cikin haɗarin yayin da waɗanda suka malaki kamfanin jiragen sama suke cewa mutane takwas sun sha a hadarin ,sai dai suna cikin wani halin mutu kwa kwai rai kwa kwai.

Mawallafi Abdourahamane Hassane

Edita Zainab Mohammed Abubakar

  (