1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wani jirgin saman yakin Isra´ila ya kai harin makami mai linzami a Gaza

August 25, 2006
https://p.dw.com/p/Bulg

Wani jirgin saman yakin Isra´ila ya kai farmaki kan wasu gine gine biyu a Zirin Gaza, inda ya jiwa mutane da dama rauni. An kai farmaki na farko kan gidan wani shugaban sojojin sa kai na kungiyar Al-Aqsa dake arewacin garin Jabaliya. Sannan na biyun kuma aka auna wani bene mai hawa biyu dake birnin Gaza. Harin ya ta da gobara wadda ta lalata ginin. Rundunar sojin Isra´ila ta yi zargin cewa ana boya makamai a cikin gine ginen sannan ta gargadi mazauna cikin su da su fice kafin kai hare-haren. A wani labarin kuma ana matsa kaimi a kokarin da ake don sako wasu ´yan jarida biyu na kasashen yamma da ake garkuwa da su a Zirin Gaza. Masu garkuwa da sun na bukatar a sako dukkan musulmi da ake tsare da su a gidajen kurkukun Amirka kafin gobe asabar. To amma ba su fadi abin da zai faru ba idan ba´a biya musu bukatun su ba. FM Falasdinawa Ismail Haniya ya yi Allah wadai da garkuwa kana ya yi kira da a sako mutanen biyu ba tare da an yi musu lahani ba.