1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wani kumbo ya nado bayanai daga duniyar Pluton

Gazali Abdu TasawaJuly 15, 2015

Duniyar Pluton ita ce falaki mafi nisa daga wannan duniya tamu da kuma aka fi jahiltarta daga cikin jerin falakun da aka sani.

https://p.dw.com/p/1Fygb
Pluto New Horizons Illustration
Hoto: JHUAPL/SwRI

Hukumar kula da binciken sararin samaniya ta kasar Amirka wato NASA ta ce wani kumbo da ta harba domin nado bayanai a kan duniyar Pluton ya yi nasarar yin hakan ta hanyar aiko da hotuna masu dauke da bayanai masu muhimmanci dangane da abun da wannan duniya ta Pluto ta kunsa. Ita dai duniyar Pluton ita ce falaki mafi nisa daga wannan duniya tamu da kuma aka fi jahiltarta daga cikin jerin falakun da aka sani.

Kumbon mai suna Sonde Spatiale New Horizon, hukumar ta NASA ta harba shi ne tun a farkon shekara ta 2006 kuma ya kusanci falakin na Pluton a karfe 11 da mintoci 48 agogon GMT bayan da ya gudanar da tafiya mai nisan sama da kilomita miliyon dubu biyar. Kudi sama da miliyon 700 ne dai hukumar ta NASA ta kashe a cikin wannan aiki .