1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wani rahoton MDD ya ce Habasha da Eritrea sun tura sojoji Somalia

October 28, 2006
https://p.dw.com/p/BueC
Wani rahoton MDD na sirri ya ce dubban dakarun kasashen Habasha da Eritrea na cikin kasar Somalia, inda suke marawa masu gaba da juna baya a fafatawar da ake yi na rike madafun iko a wannan kasa mai muhimmanci. Rahoton wanda aka fara buga shi a ranar 26 ga wannan wata ya rawaito majiyoyin diplomasiyya na kiyasin cewa dakarun Habasha kimanin dubu 6 zuwa dubu 8 na cikin kasar ta Somalia inda suke taimakon gwamnatin da kasashen duniya suka amince da ita, yayin dakarun Eritrea kimanin dubu 2 ke Somalia suna marawa kawancen kungiyoyin kotunan Islama baya. Rahoton yayi gargadin cewa katsalandan da kasashen biyu wadanda su kansu basa ga maciji da juna ke yi a harkokin cikin gidan Somalia, ka iya share fagen barkewar wani yakin basasa. Kawo yanzu jami´an MDD ba su ce uffan ba game da rahoton.