1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wani sabon faɗa ya barƙe tsakanin dakarun gwamnati da na ƙungiyar yan tawaye a ƙasar Cadi

April 29, 2010

Gwamnatin ƙasar Cadi ta bada sanarwa kashe ɗaruruwan dakarun ƙungiyar yan tawaye ta FPRN

https://p.dw.com/p/N9dQ
Idriss Deby Shugaban ƙasar CadiHoto: AP

 An bada rahoton cewa wani sabon fada ya ɓarke a ƙasar Cadi tsakanin dakarun gwamnati da na yan ƙungiyar yan' tawaye na FPRN a gabacin ƙasar da ke maƙobtaka da Sudan.Gwanatin ƙasar Cadin dai ta bada sanarwa cewa daruruwan yan tawayen suka mutu a fadan yayin da su kuma suka samu assara mutuwar soja tara.

A cikin wata sanarwa da ya baiyana ta gidan rediyo ministan watsa labarai na ƙasar ta cadi Kedallah younous, ya sheda cewa dakarun gwamnatin sun kame 80 daga cikin yan tawayen da suka samu jimuwa, to sai haryanzu ƙungiyar yan tawayen ba ta mayar da martani ba dangane da wannan furci.

Ana dai ƙara samun tashe tashe hankula a yankin ne , a dadai lokacin da ƙasar ta cadi ta cimma wata yarjejeniya tsakaninta da majalisar dinkin duniya, da ta tanadi rage adadin dakarun kiyaye zaman lafiya dake a ƙasar  daga dubu biyar zuwa 1900, saboda koken da ƙasar ta gabatar cewa ba ta bukatar sojojin majalisar dinkin duniyar.

A wannan shekara dai ƙasar ta Cadi ke shirya zaɓen yan majalisar dokoki sanan a shekara badi a gudanar da zaben shugaban kasa .

Mawallafi: Abdourahamane Hassane

Edita        Mohamed Nassiru Awal