1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Warware rikicin yajin aikin jiragen Kasa

Zainab MohammedNovember 19, 2007
https://p.dw.com/p/CJNM

Bisa ga matsin lamba daga ɓangaren gwamnatin jamus, na kawo karshen matsalar da aka fuskanta na sufuri a makon daya gabata,Kamfanin jiragen ƙasa na Deutsche Bahn da kungiyar matuka jiragen ,sun sanar dacewar shugabannin su zasu gana domin warware wannan matsalar.Yajin aikin jiragen kasar a makon daya gabata dai ya jefa jama’a cikin mawuyacin hali na tafiya wuraren ayyukansu.Ayayin da kawo yanzu kamfanin jiragen bai ce komai dangane da sauyin matsayi ba,ministan harkokin sufuri na jamus Wolfgang Tiefensee yace ya tsoma baki wajen warware matsalar.

„Akwai sabon tayi daga ɓangaren kamfanin na Deutsche Bahn wa ‚yan kungiyar,wanda ke zama wani sabon babi ne a wannan rikici.kuma bisa ga wannan tattaunawar tasu,zan yi iyakar kokari na na ganin cewar ,an samu sakamako mai tasiri na kawo karshen wannan matsala“