1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wasan ƙwallon ƙafar Afirka ya ɗauki hankalin jaridun

January 29, 2010

China kuma na faɗaɗa angizonta a nahiyar Afirka

https://p.dw.com/p/LmeP
Hoto: AP

A wannan makon ma dai jaridun na Jamus sun mayar da hankali kan nahiyar ta Afirka musamman game da gasar cin kofin ƙwallon ƙafar ƙasashen Afirka da za´a yi wasan ƙarshe ranar Lahadi tsakanin Ghana da Masar. A rahoton da ta rubuta jaridar Süddeutsche Zeitung ta fara ne da cewa wasan ƙwallon ƙafar na Afirka Cup bai yi armashi yadda aka yi zato ba.

"Tun da farkon fari harin da aka kai kan ´yan wasan ƙasar Togo gabanin fara gasar ya rage masa farin jini. Yayin da ƙasashen da za su wakilici Afirka a wasan cin kofin ƙwallon ƙafa na duniya a Afirka ta Kudu wato Nigeria, Kamaru, Ghana, Aljeriya da kuma Kodivuwa aka yi tsammanin za su zama ƙalubale ga ´yan wasan Turai da na Kudancin Amirka wajen neman cin kofin ƙwallon ƙafa na duniya, amma sun ba da kunya a Angola. Ta ce ƙananan ƙasashe kamar Gabon, Benin da Zambia sun fi sauran manyan ƙasashen da za su wakilci Afirka a wasan cin kofin duniya nuna ƙwarjini."

Har yanzu dai muna a fagen ƙwallon ƙafa inda a sharhin da ta rubuta jaridar Die Tageszeitung ta yi tsokaci ga ayar tambayar da ake sakawa kan tsaron lafiyar baƙi a Afirka Ta Kudu gabanin gasar ta duniya.

WM Südafrika 2010 Moses Mabhida Stadion in Durban
Hoto: picture alliance / dpa

"Lokaci na ƙaratowa ga gasar ƙwallon ƙafa ta duniya da za a fara cikin watan Yuni. Jaridun Afirka Ta Kudu a kullum suna mayar da hankali kan al´amuran tsaro a ƙasar. A kwanakin baya wata tashar telebijin ta shiga kanun labaru sakamakon hira da ta yi da wasu matasa waɗanda suka ce suna shirin kai hari kan baƙi da zasu je kallon wasannin na ƙwallon ƙafa. Yanzu haka dai ɗaya daga cikin matasan ya shiga hannun ´yan sanda. Jaridar ta Tageszeitung ta yaba da matakan da jami´an tsaron Afirka Ta Kudun ke ɗauke don kare ´yan kallo sannan ta yi kira ga kafofin yaɗa labaru  ƙasar da su yi takatsantsan wajen buga rahotannin masu ta da hankalin jama´a."

Ƙasar China na faɗaɗa angizonta a nahiyar Afirka, inji jaridar Rheinische Merkur inda ta ba da misali da ƙasar Ethiopia tana mai cewa: "yanzu masu ba da taimakon raya ƙasa a ƙasar dake yankin ƙahon Afirka sun samu kishiyoyi daga China. A manufofinsu na raya ƙasashe masu tasowa, Jamus da China na mayar hankalin kan Ethiopia, amma aikinsu ya banbanta. Yayin da Jamus ta dukufa wajen ba da taimakon raya ƙasa ita kuwa China ta mamaye dukkan ayyukan da suka shafi alal misali gina hanyoyin mota da dai sauransu. ´Yan ƙasar ta Ethiopia dai suna nuna ɓacin ransu domin maimakon a ɗauke su aiki, China tana tura ´ya´yanta ne suna wannan aiki, wato kenan babu wata riba ta a zo a gani da Ethiopia ke samu. Mafita daga irin wannan yarjejeniya shine maimakon bada kuɗin gudanar da aiki kamata yayi a taimakawa ƙasashen Afirka don su cike giɓin kasafin kuɗinsu."

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Edita: Yahouza Sadisou Madobi