1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

100510 WM Historie

June 2, 2010

Tarihin wasannin ƙwallon ƙafa daga farawa a ƙasar Yurogaye izuwa ƙasar Afirka ta kudu

https://p.dw.com/p/NfjU
Kofin ƙwallon ƙafa na duniya

A shekara ta 1930 aka fara gasar ƙwallon ƙafa a duniya, ƙasar farko da tara karɓar gasar itace Yurogaye, wanda kuma ta fara ɗaukar kofin duniya. Abinda yanzu ya rikiɗe yakasance wani babban abu a siyasar duniya.

Ƙungiyoyi goma sha ukku, suka hallaci gasar farko, bakwai daga ciki 'yan kudancin latin Amirka ne. Ƙungiyoyin da suka ƙware a wasa daga Turai a wacan lokacin basu samu halarta ba, ko dai sabo da banbancin siyasa, ko kuma rashin kuɗi ko kayan wasa.

A shekara ta 1934 ƙasar Italiya ta sake ɗaukar gasar, inda kuma a wannan lokacin ne Jamus ta samu kaiwa wasan ƙarshe ta samu matsayi na biyu. Bayan da Cichoslovakiya ta doke Jamusawa ci uku da ɗaya. Shekaru 20 bayan haka Jamusawa sun samu nasarar da suke jira na cin kofin duniya, a wani ƙwallon da ɗan wasansu Rahn ya zura....

Shekaru tara bayan yaƙin duniya na biyu, ƙungiyar ƙwallon ƙafan Jamus ta sake samun wannan muƙami a gasar da ƙasar Switzeeland ta karɓi baƙon cin sa. Inda suka ci ƙasar Hongire ci uku da ɗaya, wacan lokacin Kaptin Fritz Walter shine ya jagoranci 'yan wasan na Jamsu, inda yace

"Har yanzu bama iya yarda shin gaskiyane wannan abun yafaru, tsabar murna, don haka muna buƙatar wassu 'yan sa'o'i ko kwanaki, kafin wannan shauƙin ya fita daga jikinmu"

Daga nan sai ƙasar Burazil ta zama zakar ƙwallo na duniya, inda lokacin ɗan wasan Burazil Pele yake tsakiyar tashensa, abin yakai har ya kasance zakar 'yan ƙwallon ƙafa na duniya a lokacin.

A shekara ta 1966 aka buga wasan da har yanzu ake ta cece kuce kanta, inda Jamus da ƙasar Ingila mai masaukin baƙi suka buga wasan ƙarshe. An dai buga wasa har aka ƙare minti 98 babu wanda ya ci, inda ko wace ƙasa ke da ci biyu. Bayan ƙarin lokaci sai wani ɗan wasa Ingila da ake ƙira Wambley Tor ya jefa wata ƙwallo wanda ta bugi ƙarfen dake a golan ƙasar Jamus, bayan faɗawarsa wasu na cewa bata shiga layi ba, amma dai alƙalin wasa yace anci. Gottfried Dienst shi ya fura wasan, kuma ga abinda yace

"A yadda mai taimakamin dake gefe a kusada golan Jamus ya ɗaga tutarsa, ya nuna min cewa ƙwallon ya shiga ragar Jamusawa"

Wannan ya yi sanadiyar kariyar 'yan wasan Jamus, Abinda kuma ya baiwa Ingila damar ɗaukar kofi bayan ci huɗu da biyu.

Tun daga wannan lokacin ƙasashen da suka ɗauki kofin ƙwallon ƙafa na duniya, sun haɗa da Jamus a shekara ta 1974, sai Ajantina a shekara ta 1978, Italiya a shekara ta 1982, kana Ajantina ta sake cin kofin a shekara ta 1986. Jamus ta sake ɗaukar kofin a shekara ta 1990, ƙasar Burazil ta ɗau kofin a shekara ta 1994. Faransa da sau ɗaya kacal ta taɓa cin kofin, ta samu hakanne a shekara ta 1998. Sai Burazil ta sake karɓan kambunta a shekara ta 2002. Kana wasan cin kofin ƙwallon ƙafa na ƙarshe, shine wanda aka yi anan Jamus a shekara ta 2006, inda ƙasar Italiya ta lashe gasar a karo na huɗu.

Bana kuwa da gasar za ta leƙa Afirka, ko a nahiyar ta Afirka za'a samu ƙasar da za ta kafa tarihi? Da hakan kuwa yaƙara fiddo da nahiyar wanda take da 'yan wasa birjik a Turai.

Mawallafa: Usman Shehu Usman da Torsten Ahles

Edita: Umaru Aliyu