1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wasikar Guillaume Soro zuwa ga Sakatare Jannar na Majalisar Dinkin Dunai

November 30, 2005
https://p.dw.com/p/BvIg

Shugaban yan tawayen kasar Cote D´Ivoire, Guillaume Soro, ya rubuta sabuwar wasika, zuwa ga sakatare jannar na Majalisar Dinkin Dunia, Koffi Annan.

Guillaume Soro ya bukaci majalisar ta sake nazari a gam,e da hukunci da ta yanke a kwanaki baya a game da batunwsarwre rikicin kasar.

Idan ba a mata, Komitin Sulhu na Majalisa Dinkin Dunia, tare da kungiyar tarraya Afrika, sun yanke shawara cewa shugaba Lauran Bagbo, ya ci gaba da jan ragamar mulkin kasar, har lokacin da, a za a gudanar da zabe, nan da shekara guda mai zuwa, ya kuma nada saban Praminista mai cikkaken mulki.

Yan tawayen FN, take su ka yi watsi da wannan hukunci.

Guillaume ya bada shawawri guda 3 wanda a cewar sa su ne kadai ke iya hidda Coet D´Ivoire daga rikicinsiyasdar da ta ke fama da shi.

A shawara farko, ya bukaci a russa kundin tsarin mulkin kasar, a kuma nada shi a matsayin Praministan rikwan kwarya Bagbo na zaman shugaban kasa.

A shawara ta 2, ya amince ya zama mataimakin Praminista, amma da sharidin, wanda zai rike mukamin Praministan ya samu amincewa, daga bangarorin daban daban.

Sannan a shawara ta 3 kuma ta karshe ya bukaci a kirkiro kujerar mataimakin shugaban kasa, wadda kuma ,shi zai rike wannan mukami.