1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wasikar yan adawar Cote d´Ivoire ga majalisar Dinkin Dunia

Yahouza S. MadobiAugust 23, 2006

Shugabanin jam´iyun adawa a Cote d´Ivoire sun rubuta wasiƙa zuwa ga Sakatare Jannar na Majlisar Dinkin Dunia.

https://p.dw.com/p/Btya

Shugabanin Jam´iyun adawar Cote d´Ivoire, wato Tsofan shugaban ƙasa kuma shugaba Jam´iyar PDCI,Henri Konan Bedie, da tsofan Pramninista, bugu da ƙari, shugaban jam´iyar RDR Alassane Wattara, sun rubuta wasiƙar haɗin gwiwa, zuwa ga Sakatare Jannar na Majalisar Ɗinkin Dunia Koffi Annan.

Wannan wasiƙa, ta bukaci Majalisar Dinkin Dunia, ta ɗauki matakan da su ka dace, domin haramtawa shugaban ƙasa Lauran Bagbo, ƙaddamar da dokoki da su ka shafi gudanar da harakokin mulki.

Sun bayyana cewar ɗaukar wannnan mataki, kann shugaban ƙasar ya zama wajibi, ta la´akari da mummunar rawar da ya ke takawa ta fannin hanna ruwa gudu, a shirye shiryen zaɓe.

Shugabanin jam´iyun adawar, sun ɗora alhakin kon gaba kon baya, da a ke fuskanta, a shirin zaɓɓuɓukan ga shugaban ƙasa.

Sun bada misalin dokar da Lauran Bagbo ya ɗauka a ƙarshen watan da ya gabata, inda ya umurci hukumar zaɓe mai zaman kanta, ta gabatar masa da tsarin da ta tanada, a kundin zaɓe na ƙasa.

A cewar Allassane Wattara, da Henri Konan Bedie ,wannan doka ta zama shishishigi, ga ayyukan hukumar zaɓen, wanda hakan, ya saɓawa dokokin Cote d´Ivoire.

A ɗaya wajen, shugabanin 2, sun rubuta wata wasiƙa ga shugaban ƙasar Afrika ta Kudu, Tabon Mbeki, wanda shine ƙungiyar Taraya Afrika, ta naɗa, domin shiga tsakanin rikicin Cote d´Ivoire.

Sun bukaci ya tsawatawa Lauran Bagbo, a game da tarnaƙin da ya ke wa kundin tsarin mulkin ƙasa, wanda ya samu amincewa daga ɓangarori daban-daban ,bayan wata da watani na tantanawa.

Wasiƙar ta haɗin gwiwa, ta yi Allah wadai, ga passara da fadar shugaban ƙasa ta bada, a kan hanyoyin da aka tsara, na ba mutane lassisin zama yan ƙasar Cote d´Ivoire, da kuma mumunar fahintar da ta yayi ga yancin jama´iyun adawa.

Tun farkon watan da mu ke ciki, jam´iyun adawa, da yan tawayen Cote d ´Ivoire, sun buƙaci saukar Lauran Bagbo daga karagar mulki, ranar 31 ga watan Oktober, wanda shine ƙarshen wa´adin da Majalisar Ɗinkin Dunia, ta yanke masa, na zama shugaban ƙasar riƙwan ƙwarya, kamin shirya zaɓɓuɓuka.

Saidai a nasa gefe, Shugaban ya bayana cewar zai ci gaba da kasancewa kan kujera mulki, har sai ranar da a ka gudanar da zaɓen shugaban ƙasa.

A cikin watan satumber ne mai zuwa,Majalisar Ɗinkin Dunia zata shirya zaman taro, domin yanke hukunci a kan batun ci gaban Lauran Bagbo a masatyin shugaban ƙasar Cote d´Ivoire.

A wata sanarwar da ya fido a wannan laraba, wakilin musamman na Majalisar Ɗinkin Dunia, a Cote d´Ivoire, ya ce kwata- kwata ba ta yiwuwa, a shirya zaɓen a ƙasar kamin 31 ga watan oktober.