1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za'ayi mahawara kan matsayin 'yan gudun hijira

Zainab Mohammed AbubakarSeptember 8, 2015

Fraiministocin Janhuriya Czech da na Slovakia sun bayyana cewar, kasashensu ba zasu shiga dukkan wata yarjejeniya ta daukar nauyin 'yan gudun hijira ba

https://p.dw.com/p/1GSat
Bohuslav Sobotka Robert Fico Werner Faymann Bratislava
Hoto: picture-alliance/dpa/Vaclav Salek

A yayin wata ganawa ta fraiminista Bohuslav Sobotka na Jaqnhuriyar Czech da Robert Fico na Slovakia da kuma takwaransu na Ostiriya Werner Faymann a birnin Bratislava, shugabannin biyu sun bayyana rashin dacewar matsayin hukumar gudanarwar Tarayyar Turai, inda suka ce bai kamata a tilastawa kowa daukar nauyin 'yan gudun hijirar ba, a bar ko wace kasa ta dauki matakin kashin kanta na amincewa ko kin amincewa da 'yan gudun hijirar.

Dubban 'yan gudun hijira ne dai ke ci gaba da yin tururuwa zuwa birnin Munich da ke nan Tarayyar Jamus. Gwamnan yankin Bavaria Christoph Hillenbrand ya kiyasta cewar, a jiya Litinin kadai kimanin mutane dubu 10 suka isa yankin, daura da wasu dubu 20 da suka samu nasarar shigowa cikin kasar a karshen mako.

A mako mai zuwa nedai ministocin harkokin cikin gida na Tarayyar Turai zasu yi taron mahawara dangane da rarraba 'yan gudunn hijirar tsakanin kasashen na EU.