1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wasu sojojin Amirka sun nemi mafakar siyasa a kasar Kanada

Mohammad Nasiru AwalJuly 21, 2004
https://p.dw.com/p/Bvhs
Sojojin Amirka a Iraqi
Sojojin Amirka a IraqiHoto: AP

Brandon Hughey na da shekaru 17 a duniya lokacin da aka dauke shi aikin soja a rundunar sojin Amirka. Ya yi zaton hakan wata dama ce da zata samar masa kudin da yake bukata don neman karin ilimi a jami´a. To amma yanzu tun ba a yi shekara biyu ba murnarsa ta koma ciki, saboda ya gudu daga soja, sakamakon adawar da ya nuna da yakin kasar Iraqi.

"Shugaba Bush ya karya dokokin kasa da kasa, saboda haka kamata ya yi ko-wane soja ya nuna adawa da hakan. A lokacin da na fadawa shugaba na cewar zan bar aikin soja, sai ya ce da ni ai ba ni da wani zabi face in ci gaba da wannan aiki."

A farkon wannan shekara Brandon Hughey ya tsallaka zuwa birnin Ontario na kasar Kanada inda ya nemi mafakar siyasa. Ba shi kadai ne sojan Amirka da ya bi ta wannan hanya don kauracewa yakin Iraqi ba. To sai dai ba za´a iya kwatanta halin da ake ciki yanzu da wanda aka samu a cikin shekarun 1960 ba, lokacin da dubban sojojin Amirka suka gudu zuwa makwabciyar kasar don kauracewa yakin kasar Vietnam. To sai dai yawan sojojin dake gudu daga aikin soja a yanzu yana karuwa.

Jeremy Hinzman sojan leman Amirka shi ma yanke shawarar tserewa zuwa Kanadar don nuna adawa da yakin Iraqi.

"Rayuwa ta dai ba wata aba ce ta musamman ba. Amma kuma darajarta ta fi in kyale haka kaiwa a tura ni inda za´a kashe ni ko kuma in kashe wadanda ba su ji ba su gani ba. Ina fata zamu iya tafiyar da rayuwar mu a nan ba da wata tsangwama ba."

Ga rundunar sojan Amirka dai duk sojan da ya gudu kamar Hughey da Hinzman to ya na iya fuskantar hukuncin kisa, to amma bisa ga dukkan alamu hukuncin da za´a yanke musu har in dai sun koma Amirka ba zai wuce daurin wasu ´yan shekaru a gidan kurkuku ba. Hakan dai ka iya faruwa ne idan Kanada ta ki ba su mafakar siyasa kuma to koma da su Amirka. Amma lauyarsu Jeffrey House na da kyakkyawan fatan cewa za´a ba sojojin biyu izinin zama cikin Kanada.

A ´yan shekarun da suka wuce Kanada ta tsananta dokokin ba da mafaka a cikin kasar, kuma yanzu kome ya canza ba kamar a da ba ne lokacin da aka ba sojojin da suka kauracewa yakin Vietnam mafaka a cikin Kanada. A saboda haka wata masaniyar kimiyar dokokin kasa da kasa a jami´ar Toronto, Audrey Macwin ta nuna shakku game da nasarar samun mafakar siyasa musamman ga Amirkawan.