1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wasu ’yan bindiga sun halaka mabiya ɗariƙar shi’iti 20 a birnin Bagadaza.

August 20, 2006
https://p.dw.com/p/Bum8

Rahotannin da muka samu daga birnin Bagadazan Iraqi sun ce wasu ’yan bindiga sun halaka mutane 20, mabiya ɗariƙar shi’iti da ke jerin gwano zuwa maƙabartar wani shahararren shugabansu, Imam Musa Kadhim. Rahotannin sun ce ’yan bindigan sun buɗe wuta cikin jama’a ne daga kan rufin gidajen da ke kewayen. Jami’an gwamnatin Iraqin sun ce, ’yan sandan ƙasar sun bindige ’yan bindiga huɗu a wata musayar wutar da suka yi da su. Kazalika kuma, sun ce fiye da mutane ɗari 2 da 50 ne suka ji raunuka yayin da suke ƙoƙarin tserewa daga inda rikicin ya ɓarke.

An dai hana duk wata zirga-zirgan motoci a birnin Bagadazan, har tsawon yini biyu, yayin da ake bikin mabiya ɗariƙar shi’itin.