1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wata kungiyar yan tawaye a Darfur tace ta shirya tattaunawa da gwamnati

October 19, 2006
https://p.dw.com/p/BufJ

Shugabanin wata sabuwar kungiyar yan tawayen Darfur sunce kungiyar a shirye take ta tattauna da gwamnatin Sudan,sai dai kuma ta bukaci yancin cin gashin kai na yankin.

Kungiyar yan tawaye daya ce kadai ta sanya hannu akan yarjejeniyar zaman lafiya ta watan mayu,wadda sauran kungiyoy 3 da kuma dubban jamaar Darfur sukayi watsi da ita,suna masu korafin cewa bai bada diya da ake bukata ko wakilce da ya kamata ga yan Darfur din ba.

Wani babban memba na kungiyar ta NRF wadda aka kafa biyowa bayan yarjejeniyar ta Abuja,Khalil Ibrahim yace suna bukatar samarda yarjejeniya,kamar wadda aka cimmawa bayan yakin basasa tsakanin arewaci da kudancin kasar,wadda ta baiwa kudancin sudan yancin cin gashin kanta tare da yancin gudanar da kuriar raba gardama akan ballewa a 2011.

Ministan harkokin wajen Sudan Lam Akol yace har yanzu gwamnati bata karbi wannan takardar bukata ta yan tawayen ba.

Gwamnatin Sudan din dai tunda farko tayi watsi da batun ballewar yankin Darfur.