1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wata sabuwar girgizar kasa ta auku a kasar Pakistan

November 6, 2005
https://p.dw.com/p/BvML

Kusan wata daya bayan aukuwar mummunar girgizar kasa a kudancin Asiya wata sabuwar girgizar kasar ta auku a kasar Pakistan. Hukumomi sun ce karfin wannan girgizar kasar ya kai awo 6 a ma´aunin Richter kuma ta kasance mafi muni a cikin jerin girgizar kasar da aka fuskanta bayan ta ranar 8 ga watan oktoba. Hukumomin sun kara da cewa girgizar kasar ta fi karfi ne a wani yanki mai nisan kilomita 120 arewa da Islamabad babban birnin kasar. Daukacin mazauna wannan yankin a cikin tsoro sun tsere daga gidajen su da kuma sansanonin da suka samu mafaka tun bayan aukuwar girgizar kasar ranar 8 ga watan oktoba, wadda ta halaka mutane dubu 73 a kan iyakar Pakistan da Indiya.