1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wata sabuwar guguwa ta ratsa kasar Haiti mai fama da matsalolin talauci

October 25, 2005
https://p.dw.com/p/BvNw

Wata sabuwar mahaukaciyar guguwa da aka yiwa lakabi da Alpha ta halaka mutane 11 sannan ta yi kaca-kaca da gabar tekun tsibirin Haiti. Kamar yadda wadanda suka shaida abin da ya faru suka nunar guguwar hade da ruwan sama kamar da bakin kwarya sun haddasa mummunar barna a wannan kasa dake jerin kasashen duniya mafi talauci. A kuma halin da ake ciki mahaukaciyar guguwar Wilma wadda yanzu haka take gudun kilomita 200 cikin awa daya ta ratsa yankin jihar Florida. Hukumomi a jihar sun ce akalla mutane 6 sun rasu.